Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Jihar Katsina cikin gaggawa ya amshi ƙorafin al’ummar Barhim, har ya bada umarnin fidda magudanan ruwa a bisa sabon aikin tagwayen hanyoyi daga Barhim zuwa sabuwar hanyar “Estern Bye Pass”.
Bayan ganin ƙorafin al’ummar Barhim da ke cikin ƙaramar hukumar Batagarawaa Jihar Katsina, na ambaliyar ruwa sanadiyar rashin magudanan ruwa akan aikin tagwayen hanyoyi da tsara unguwar Barhim.
Cikin gaggawa gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi umarnin fidda magudanan ruwa akan aikin tagwayen hanyoyin domin kare al’ummar Barhim daga ibtala’in ambaliyar ruwa duba da yanayin damina da aka shiga.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, wanda ya yi sanadiyar afkuwar ambaliyar ruwa a unguwar Barhim saboda rashin magudanan ruwa akan sabon aikin tagwayen hanyoyin.
Yanzu haka kamfanin dake aikin gina tagwayen hanyoyin, ya fara ginin magudanan ruwan, kamar yadda gwamnan jihar ya basu umarni a bisa buƙatar al’ummar Barhim.
A na sa ran aikin magudanan ruwa zai bazu zuwa sassan jihar.
