Daga: SHEHU MUSTAPHA CHAJI
Hukumar raya kogunan Hadejia Jama’are (HJRBDA) ƙarƙashin jagorancin Injiniya Dakta Rabiu Suleiman Bichi tana da mafi girman tsarin ban-ruwa mai aiki a cikin hukumomin raya koguna 12 na Najeriya. Tun bayan hawansa mulki tare da manyan jami’ansa irin su Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, Daraktan Kuɗi da Gudanarwa, Bichi ya sha bayyana cewa sauye-sauyen da yake yi a HJRBDA sun yi daidai da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope Agenda, musamman a fannin tsaron abinci.
Yayin da ‘yan Nijeriya ke bikin cikar shekaru 3 na gyare-gyare ƙarƙashin Renewed Hope Agenda, HJRBDA ƙarƙashin Rabiu Suleiman Bichi ta samu nasarori masu yawa a fannin ban-ruwa, sarrafa ambaliya, noma da tsaron abinci.
Daidai da manufofin Shugaba Tinubu, Bichi ya mayar da hankali wajen faɗaɗa ban-ruwa, gyara madatsun ruwa, ƙarfafa matasa a noma, tsaftace magudanan ruwa, da yaƙi da ciyawar Typha da ambaliya.
Ayyukan HJRBDA ƙarƙashin Engr. Bichi sun taimaka wajen haɓaka samar da abinci a jihohin Kano, Jigawa da Bauchi, tare da zama ginshiƙi wajen aiwatar da Renewed Hope Agenda a Arewacin Nijeriya.
Wasu daga cikin manyan nasarorin da aka samu:
- Gyara da faɗaɗa madatsun ruwa 16a Kano ciki har da Tiga, Goje da Kafin Chiri don tallafawa noman rani duk shekara.
- Farfaɗo da aikin madatsar ruwa ta Kafin Zaki a Bauchi bayan shekaru 40 da dakatar da ita.
- Ci gaba da gina madatsar ruwa ta Malikawa Garu tare da buɗe hekta 6,000 na filayen noma.
- Ci gaba da gina madatsar ruwa ta Dunbulum a Tsanyawa, Kano.
- Ƙaddamar da aikin madatsar ruwa ta Bela a Bichi, Kano.
- Ayyukan magudanan ruwa da yaƙi da zaizayar ƙasa a Jahun, Jigawa.
- Sanya rijiyoyin burtsatse 40 don samar wa Dutse ruwa mai tsafta.
- Shirye-shiryen samar da megawatt takwas na lantarki tare da ban-ruwa da kiwon kifi a madatsar Tiga.
- Yaƙi da ciyawar Typha: Bichi ya ayyana “halin gaggawa” kan Typha. An fara tsaftacewa duk shekara wanda ya dawo da ruwa ga dubban manoma kuma ya rage ambaliya a Jigawa da Bauchi.
- Horar da matasa 5,000 kan dabarun noma na zamani kamar drip irrigation da greenhouse a sabuwar cibiyar horo ta HJRBDA a Kano.
- Tallafawa shirin “Every Home a Garden” na Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sen. Oluremi Tinubu, don ƙarfafa noman lambuna a gidaje.
- Hanyoyi da tsaro: Gina hanyoyin shiga gonaki a Tudunwada Galala, Ningi, Bauchi. Kammala Makarantar Horar da NSCDC a Gwarzo, Kano don ƙarfafa tsaro.
- Ci gaba da samar da rijiyoyin masana’antu a Kano, Jigawa da Bauchi.
- Haɗin gwiwa da sauran hukumomi don haɓaka noma a Arewa maso Yamma.
- Ƙaddamar da tsarin drip irrigation a Kano da Jigawa.
- Kammala ayyukan ruwa 12 a harabar Jami’ar Bayero Kano.
- Sulhunta rikice-rikicen shekaru tsakanin ƙungiyoyin nasu amfani da ruwa WUA a Kano, Jigawa da Bauchi.
Ta hanyar mayar da HJRBDA hukuma mai inganci, jagorancin Rabiu Suleiman Bichi ya samar da dandali mai ƙarfi don ƙarfafa manufofin Shugaba Tinubu a Kano, Jigawa, Bauchi da Arewa baki ɗaya.
Shehu Chaji ya rubuta daga Kano
