Gwamnatin Nasarawa ta ƙaryata zargin Maku kan shirin maguɗin zaɓe

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana zargin da ɗan takarar kujerar sanata a Nasarawa ta Arewa a jam’iyyar Labour Party Labaran Maku ya yi kan shirin jam’iyya mai ci a jihar na tafka maguɗin zaɓe a matsayin mara tushe.

Babban mataimakin gwamnan kan harkokin jama’a Hon. Peter Ahemba ne ya faɗi haka yau Juma’a a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar NUJ dake Lafia babban birnin jihar.

Idan za a iya tunawa Labaran Maku wanda tsohon mataimakin gwamna ne kuma tsohon ministan yaɗa labarai ya bayyana a ranar Laraba a Akpata na ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon cewa APC ta ware mazaɓu tara domin tafka maguɗin zaɓe kuma gwamna Abdullahi Sule na aiki tare da ‘yan sanda domin sauya manyan jami’an tsaro kafin zaɓen cike gurbin da za a yi a ranar 20 ga Yuni da ake ciki.

Ahemba ya ƙaryata zargin gaba ɗaya yana cewa gwamna Sule bai taba ba da umarni ko ƙarfafa tsoma baki a kowanne zaɓe ba tun daga shekarar 2019.

“Waɗannan zarge-zarge ba wai siyasar nuna kyama ba ne kawai har ma nuni ne na cewa ɗan takara ya firgita ne saboda matsayinsa nai rauni a tsakanin masu neman zaɓen ” in ji Ahemba.

“A bayyane yake cewa Maku ya sha kaye a duk zaɓen da ya tsaya shi kaɗai. Sai dai zai iya cewa ya yi nasara ne a haɗin gwiwa da gwamna na farko da aka zaɓa ta hanyar dimokradiyya wato Sanata Abdullahi Adamu.”

Me taimaka wa gwamnan yace zargin cewa ana sauya shugabannin rundunar ‘yan sanda domin taimakawa wajen cin zaɓe ba shi da tushe. Yace aikin tura ‘yan sanda na ƙarƙashin iko na tsari na babban sufeton ‘yan sanda ne.

Ya ƙalubalanci Maku ya gabatar da wata shaida ga INEC ko hukumomin tsaro maimakon yin zarge-zarge a kafafen yaɗa labarai.

Ahemba ya kuma soki shawarar Maku cewa ƙorafe-ƙorafe kan zaɓe na iya haifar da rashin tsaro yana mai kira ga ‘yan sanda su ɗauki Maku idan tashin hankali ya ɓarke.

“Mutanen Nasarawa ta Arewa sun cancanci samun tsari mai lumana da tsari kuma gwamnati ta himmatu wajen aiki tare da dukkan hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaɓe mai lumana a ranar 20 ga Yuni 2026,” inji shi.

Ahemba ya ce gwamnatin Sule ta kasance tana girmama ƙa’idojin dimokuraɗiyya da samun zaɓe mai lumana kuma an bai wa ‘yan jam’iyyu daban-daban damar fito da wakilansu a matakan jihar da na ƙasa tun 2019.

Ya tabbatar wa masu zaɓe a Akwanga da Nasarawa Eggon da Wamba duk a Arewacin jihar cewa za a ɗauki ƙuri’arsu da muhimmanci kuma hukumomin tsaro za su kare su kafin lokacin da kuma bayan zaɓen.

“Gwamnati na ci gaba da tattaunawa da sarakuna da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa domin inganta zaman lafiya.

An bar kujerar sanata ta Nasarawa ta Arewa ne ga ‘yan takaran bayan mutuwar sanatan da ya rike ta wato marigayi Sanata Godiya Akwashiki ya rasu, sannan INEC ta sanya ranar 20 ga Yuni 2026 domin gudanar da zaɓen cike gurbin.

By ukarofi

Leave a Reply