Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Kotun Tarayya da ke Legas ta bayyana cewa yunƙurin da Majalisar Dokokin Nijeriya ke yi na sayen motocin da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 110 da wasu alawus-alawus ya saɓa wa ƙa’idar sayen kayayyaki na gwamnati da tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da yardar al’umma.
A cikin jawabin da cibiyar kare haƙƙin al’umma da tattalin arziƙi da ayyukan gwamanati (SERAP) ta raba wa manema labarai, ta ce, mai shari’a Yellim Bogoro ya bayyana cewa shirin kashe Naira 40 kan sayen motoci 465 ga ‘yan majalisar tarayya da tallafin Naira biliyan 70 a matsayin kuɗin alawus-alawus ga sabbin ‘yan majalisar da aka zaɓa ya saɓa wa doka da kuma tsarin sayen kayayyaki na gwamnati.
ƙarar mai lambar FHC/L/CS/1606/2023 da ƙungiyar SERAP ta shigar a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.
A yayin da yake yanke hukunci a ranar 6 ga watan Mayu, Bogoro ya ba da umarnin cewa lallai ne shugaban majalisun da su tabbatar da cewar an bi tsarin da gwamnati wajen sayen kayayyaki ta hanyar bin hanyoyin da suka kamata kuma tsarin ya kasance a buɗe kuma darajar kayan su yi daidai da na kuɗin.
“Tsarin rarrabe iko ba yana katange majalisar ne da ba ta damar aikata haramtaccen abu ne” in ji mai shari’ar yana mai jaddada cewa damuwar kotu shi ne halasci da bin tanadin kundin tsarin mulki wajen kashe kuɗin majalisa.”
Kotun ta fahimci cewa ‘yan majalisar su ne za su ci moriyar kashe kuɗin da suka amince da shi wanda ya jefa su cikin halin da ya ci karo da muradan al’umma.
“Waɗanda za su ci moriyar kashe kuɗin su ne masu amincewa da kuɗin kuma kai tsaye kuɗin ya shafi sayen kayayyaki. Wannan ya ƙunshi batu na ƙashin kai da cin karo da muradai,” inji Bogoro.
La’akari da irin wannan batu, mai shari’a ya ce ware Naira biliyan 110 da ‘yan majalisa suka yi na zuwa ne a lokacin da al’umma ke cikin mawuyacin hali.
“Na yi la’akar halin tattalin arziƙi a Nijeriya da kuma wahalar da ‘yan Nijeriya ke ciki.
La’akari da haka, ware Naira biliyan 110 domin amfanin ‘yan majalisa na nuna gaza fifita muradan Nijeriya, a cewar mai shari’a.
Kotun ta ƙara bayyana cewa, kashe kuɗin ya ci karo da alƙawarin da ‘yan majalisa suka ɗauka na muƙaman da suke riƙe da su.
Mai shari’a Bogoro ya yi watsi da ƙalubalantar farko na hukuncin da kotun ta yi da matakin da SERAP ta ɗauka. Ya yanke hukuncin cewa, dokikin Nijeriya sun amince da hukunci idan ya ci karo da ra’ayin al’umma cewa SERAP ta yi koke ne kan abin da ya shafi muradan al’umma.
A kan wannan al’amari, mai shari’a ya bayyana cewa waɗanda ake ƙara sun gaza ba da sahihancin hukunci da ke nuna ba su saɓa wa tanadin sayen kayayyaki na gwamnati ba da tanade-tanaden neman kwangila da auna kuɗi da darajar kayan kamar yadda dokar sayen kayayyaki na gwamnati.
Sakamokon haka, kotun ta bayyana cewa ƙudurin sayen ababen hawa da guda 465 da aka ware wa Naira biliyan 40 sun saɓa wa doka da tanadin kundin tsarin mulki da kundin ɗa’ar ma’aikata a yayin da ya ba da umarnin tabbatar da an bi doka da yin gaskiya da auna kuɗi da darajar kuɗin kayan da za a siya.
Wannan mataki na shari’a ya samo asali ne daga shirin majalisa karo na 10 da ke shirin sayen ababen hawa a yayin da Nijeriya ke fama da matsalar tattalin arziƙi bayan cire tallafin man fetur.
SERAP ta ƙalubalanci ‘yan majalisar kan shirin kashe Naira biliyan 70 a matsayin tallafin alawus-alawus ga sabbin ‘yan majalisa da kashe Naira biliyan 40 domin sayen motoci a yayin da aka ware Naira biliyan 500 domin raba wa miliyoyin talakawan Nijeriya waɗanda suka ke fama da tsadar rayuwa.
SERAP ta nemi Akpabio da Abbas da su rage kuɗin da suka ware wajen sayen ababen hawan da soke ƙarin kasafin kuɗin da ware na Naira biliyan 110.
ƙungiyar ta ce kashe kuɗin ya saɓa wa kundin dokokin sayen kayayyaki na gwamnati da kundin ɗa’ar ma’aikata da rantsuwar da ‘yan majalisar suka yi na kare kundin tsarin mulkin Nijeriya.
