Ranar Dimukraɗiyya: Tinubu yana gina ƙwaƙƙwarar Nijeriya ta kowa da kowa – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniyar gina Nijeriya mai ƙwari, wadda ta haɗa kowa da kowa, kuma mai wadata, inji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris.

Ya faɗi haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron manema labarai da aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026.

Idris ya ce, “Bikin Ranar Dimokiraɗiyya na wannan shekarar yana da muhimmanci ta musamman domin ya zo daidai da cikar shekara uku na gwamnatin Sabunta Fata. Wannan dama ce ta yin bitar irin cigaban da ƙasa ta samu, tantance tasirin sauye-sauyen da ake aiwatarwa, da kuma sabunta ƙudirin mu na gina Nijeriya mai ƙarfi da haɗin kai.”

Ya bayyana cewa Ranar Dimokiraɗiyya tana ci gaba da kasancewa wata muhimmiyar rana ta yin nazari kan tafiyar dimokiraɗiyyar Nijeriya, murnar juriyar cibiyoyin dimokiraɗiyya, da kuma girmama sadaukarwar jaruman ƙasa da suka yi gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimokiraɗiyya a ƙasar nan.

Ya ce, “Ranar Dimokiraɗiyya tana da matsayi na musamman a kalandar ƙasar mu. Tana ba mu damar waiwayen tafiyar dimokiraɗiyyar mu, murnar juriyar cibiyoyin mu, da kuma girmama sadaukarwar jaruman ƙasa da suka tsaya tsayin daka wajen fafutukar tabbatar da mulkin dimokiraɗiyya.”

Ministan ya kuma karrama .arigayi Bashorun Moshood Kashimawo Olawale (M.K.O.) Abiola da sauran jaruman dimokiraɗiyya, waɗanda sadaukarwar su ta taimaka wajen tabbatar da ’yancin dimokiraɗiyyar da ’yan Nijeriya suke mora a yau.

Haka kuma ya yaba da gudunmawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran masu fafutukar dimokiraɗiyya da suka taka muhimmiyar rawa wajen dawo da kuma ƙarfafa mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya.

Idris ya bayyana shekaru 27 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya ba tare da tangarda ba a matsayin babbar nasara ta ƙasa, kuma hujja ce ta juriyar al’ummar Nijeriya, ƙudirin su da kuma burin su na tabbatar da dimokiraɗiyya.

Ya ce, “Shekaru ashirin da bakwai na mulkin dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba wata babbar nasara ce da ta cancanci a yi murna da ita. Wannan shaida ce ta jajircewar ’yan Nijeriya wajen kare darajojin dimokiraɗiyya, ƙarfafa cibiyoyin ƙasa, da kuma ci gaba da neman gina ƙasa mai wadata da haɗin kai.”

Ministan ya ƙara da cewa bikin Ranar Dimokiraɗiyya na bana ya fi samun muhimmanci saboda ya zo daidai da cikar shekara uku na gwamnatin Sabunta Fata, wanda ke ba ’yan Nijeriya damar tantance ci gaban ƙasa, nazarin tasirin sauye-sauyen da ake aiwatarwa, da kuma sabunta ƙudirin su na ci gaban ƙasa.

A cewar sa, gwamnatin na ci gaba da mayar da hankali wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokiraɗiyya, inganta haɗin kan ƙasa, faɗaɗa damar tattalin arziki, da samar da cigaba mai ɗorewa ga dukkan ’yan Nijeriya ta hanyar aiwatar da Ajandar Sabunta Fata.

Ya bayyana cewa an shirya taron manema labaran ne domin bai wa ’yan Nijeriya da al’ummomin duniya damar fahimtar tafiyar gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata, tare da bayyana manyan nasarorin da aka samu, ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma hangen nesan da ke jagorantar manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Ministoci na Shirya Bukukuwan Ranar Dimokiraɗiyya ta 2026, ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen taron, ya bayyana shekaru 27 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba a matsayin wata babbar nasara ta ƙasa da ke nuna juriyar al’ummar Nijeriya da cibiyoyin dimokiraɗiyya.

Sanata Akume ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar wa da ’yan Nijeriya amfanin da za su gani a zahiri ta hanyar Ajandar Sabunta Fata, yana mai cewa sauye-sauyen da aka aiwatar a muhimman sassan tattalin arziki sun fara haifar da sakamako mai ma’ana.

Ya ce, “Matakan manufofin da wannan gwamnati ta ɗauka, ciki har da cire tallafin man fetur da gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje, sun kasance masu wahala amma wajibi. Sun samar da damar kuɗaɗe don saka hannun jari a muhimman fannoni kamar ababen more rayuwa, shirye-shiryen tallafa wa al’umma, ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa tattalin arziki. Yayin da kuɗaɗen shiga ke ƙaruwa kuma tattalin arziki ke samun daidaito, ’yan Nijeriya za su ƙara ganin amfanin waɗannan sauye-sauye.”

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli, Injiniya Farfesa Joseph Terlumun Utseɓ; ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Uba Maigari; Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga; Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwar Manufofi, Daniel Bwala; Sakatarorin Dindindin; shugabannin hukumomi da sauran manyan baƙi.

By ukarofi