Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Malam Falaki Network of Africa (FNA), wadda ta haɗa masu nazarin taurari da wasu malaman addini, ta yi hasashen cewa babban zaɓen Nijeriya na shekarar 2027 na iya fuskantar tashe-tashen hankali, yaɗuwar bayanan ƙarya da rikice-rikicen siyasa.
Shugaban ƙungiyar, Imam Habib Abdulkarim Assufiyyu, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Talata.
A cewarsa, nazarin da ƙungiyar ta gudanar ya nuna akwai buƙatar a dage da addu’o’i da neman taimakon Allah kafin da lokacin gudanar da zaɓukan da aka tsara yi a shekarar 2027.
Ya ce hasashen nasu yana da nasaba ne da nazarin da suka gudanar kan ababen da ke gudana a sararin samaniya da tsarin taurari da sauran bayanan da suka shafi ilimin falaki.
“Bincikenmu ya nuna akwai buƙatar yin addu’o’i na musamman domin tabbatar da cewa zaɓukan da za a gudanar sun gudana cikin lumana da nasara,” inji Assufiyyu.
Ya yi zargin cewa, tsarin da wasu taurari za su kasance a ranar 16 ga Janairu, 2027, wanda ya haɗa da abin da ya kira Venus-Mars sƙuare da Mercury-Pluto conjunction, na iya haifar da yanayi da ake dangantawa da tashin hankali tsakanin jama’a da shugabannin siyasa.
Ya bayyana cewa hakan na iya ƙarfafa muhawarar siyasa mai zafi, yaɗuwar jita-jita da saƙonnin rarrabuwar kai.
“A taƙaice, ranar 16 ga Janairu na ɗauke da haɗarin ƙaruwa na muhawara mai zafi, rikice-rikicen siyasa, rashin haɗin kai da kuma matsalolin zaman lafiya, musamman idan aka yi la’akari da tarihin zaɓe a Nijeriya,” inji shi.
Shugaban FNA ya kuma nuna damuwa kan wani yanayi na musamman da ake sa ran zai faru a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, wanda ya haɗa da cikakken wata da kuma kusufin wata mai rauni, wato penumbral lunar eclipse.
Ya ce ana danganta irin wannan yanayi da sauye-sauye na bazata, matsalolin tsaro, zanga-zangar jama’a da kuma ƙalubalen haɗin kan al’umma.
“Saboda waɗannan alamomi, Falaki Network ta yi imanin cewa babban zaɓen Nijeriya na 2027 zai gudana ne a ƙarƙashin yanayin taurari da ke buƙatar addu’ar gama-gari da kuma ƙara himma ta ruhaniya,” inji shi.
ƙungiyar ta kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su yi addu’o’i domin samun zaman lafiya da nasarar gudanar da zaɓe cikin lumana.
Baya ga batun zaɓe, FNA ta ba da shawarar a riƙa la’akari da abin da ta kira “dacewar taurari” tsakanin ma’aurata kafin aure, tare da ba da shawarar a nemi rahotannin tantancewa daga masu ilimi a wannan fanni.
Ta kuma shawarci shugabannin addinai da su ƙarfafa masu shirin aure su nemi takardar tantance dacewar taurari, tana mai cewa hakan na iya taimakawa wajen gano wasu ƙalubale kafin aure.
“Kamar yadda ake yin gwajin rukuni na jini da na ƙwayoyin halitta (genotype), muna ba da shawarar ma’aurata su nemi tantancewar dacewar taurari daga ƙwararru,” inji Assufiyyu.
Har ila yau, ƙungiyar ta yi kira ga masu magungunan gargajiya da masu bincike su yi nazari kan yiwuwar amfani da bayanan ilimin taurari a wasu fannoni na bincike domin gano tushen wasu cututtuka da inganta sakamakon magani.
ƙungiyar ta ce a shirye take ta yi haɗin gwiwa da masu bincike, ɗalibai da sauran masu sha’awar ilimin falaki da al’adun gargajiya domin ci gaban al’umma.
