Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta sanar da cewa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne zai jagoranci babban taron ƙasa kan harkokin tsaro da ƙungiyar za ta gudanar a Abuja.
Shugabar Kwamitin Shirya Taron, Kwamared Abimbola Oyetunde, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, inda ta ce taron zai taimaka wajen kara dankon hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.
Ta ce za a gudanar da taron na kwanaki biyu ne daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Yunin 2026, karkashin taken “Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro a Matsayin Abokan Hulɗa Wajen Gina ƙasa.”
A cewarta, an shirya taron ne domin samar da wata babbar kafa ta tattaunawa tsakanin ’yan jarida da jami’an tsaro kan hanyoyin da za su kara yin aiki tare wajen kare kasa, da kuma yadda za a rika sarrafa bayanai cikin kwarewa yayin lokutan rikice-rikice da matsalolin tsaro.
Ta kara da cewa taron zai hada manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomin tsaro, editoci, shugabannin kafafen yada labarai, kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Nijeriya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, za su halarci taron a matsayin manyan baki na musamman.
Haka kuma, Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, ne zai gabatar da muhimmin jawabin taron, yayin da Shugaban Kasa na NUJ, Kwamared Alhassan Yahya, zai kasance mai masaukin baki.
Oyetunde ta bayyana cewa taron na zuwa ne a lokacin da Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro iri-iri, yawaitar yada labaran karya da kuma fargabar jama’a kan batutuwan da suka shafi tsaro.
Ta ce ƙungiyar ta yi imanin cewa ingantacciyar mu’amala tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro na da matukar muhimmanci wajen inganta sadarwa a lokutan rikici, dakile yada bayanan karya da tabbatar da cewa jama’a sun samu sahihan bayanai cikin lokaci.
A cewarta, za a kammala taron ne da fitar da sanarwar karshe da kuma tsara hanyoyin ci gaba da hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin tsaro a nan gaba.
Kungiyar NUJ ta sake jaddada kudirinta na kare ’yancin aikin jarida, bin ka’idojin sana’a, da kuma inganta walwala da tsaron ’yan jarida a fadin kasar nan.
Ta kuma bayyana cewa duk da rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen sa ido kan ayyukan gwamnati, akwai bukatar su ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin kare rayuka, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya a Nijeriya.
