’Yan kasuwar katako na fatan Abba zai inganta kasuwar Rijiyar Lemo – Aikawa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Kwamared Shehu Inuwa Aikawa ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya kara mayar da hankali wajen inganta kasuwar katako ta Rijiyar Lemo domin ta zama daya daga cikin manyan kasuwannin katako mafi inganci a Nijeriya.

Aikawa ya ce gwamnatin jihar na da kudurin tabbatar da cewa Kano ta ci gaba da zama abin koyi wajen gudanar da ayyukan raya kasa, musamman karkashin manufar “Kano First”.

Ya bayyana cewa akwai bukatar a gyara hanyoyin shiga da fita, magudanan ruwa da sauran muhimman ababen more rayuwa a kasuwar domin saukaka harkokin kasuwanci da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

Ya ƙara da cewa kasancewar kasuwar ta katako ce, akwai bukatar daukar matakan kariya daga haɗurran gobara da sauran matsaloli da ka iya tasowa.

Aikawa ya kuma yaba wa Ma’aikatar ƙananan Hukumomi ta jihar da shugabannin kananan hukumomi bisa ƙoƙarin tabbatar da bin doka da oda wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya kammala da yabawa shugabannin kasuwar katako ta Rijiyar Lemo saboda yadda suke tafiyar da harkokin kasuwar cikin zaman lafiya da hadin kai.

By ukarofi

Leave a Reply