Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zamanin da gwamnati ke fara ayyuka sannan a bar su ba a kammala ba ya wuce, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala dukkan ayyukan da ta fara ko kuma ta gada daga gwamnatocin baya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da manyan titunan Outer Southern Eɗpressway (OSEɗ) daga mahadar Ring Road I zuwa Ring Road II a Abuja. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya wakilce shi a wajen taron.
A cewarsa, gwamnatinsa ba ta da manufar fara ayyuka ta bar su a baya.
“Ba ma fara ayyuka domin mu yi watsi da su. Zamanin ayyukan da ba a kammala ba a Nijeriya yana ƙarewa. Muna kammala ayyukan da muka fara, har ma da waɗanda ba mu fara ba,” inji shi.
Shugaban ya ce lokacin da ya hau mulki ya yi alƙawarin kawo sauyi mai ma’ana ta hanyar aiwatar da ayyukan da jama’a za su gani kuma su amfana da su kai tsaye.
Ya bayyana cewa aikin titin OSEɗ ba kawai gina hanya ba ne, illa wata hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga ga mazauna babban birnin tarayya.
Tinubu ya ce ingantattun hanyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a harkokin sufuri.
Ya tunatar da cewa gwamnatinsa ta gada aikin OSEɗ wanda ake aiwatarwa a matakai daban-daban, inda aka kaddamar da sashe na farko daga Villa Roundabout zuwa Ring Road I a shekarar 2024, sannan aka buɗe titin gefen hagu mai tsawon kilomita 15 a shekarar 2025.
A cewarsa, sabon sashe da aka ƙaddamar yanzu zai ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci tare da faɗaɗa ci gaban Abuja.
Shugaban ya yaba wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen sauya fasalin Abuja ta hanyar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
“Minista Wike ya nuna cewa aikin gwamnati ya ta’allaka ne a kan sakamako ba uzuri ba. Ya tabbatar da cewa an ci gaba da ayyuka kamar yadda aka tsara,” inji Tinubu.
Ya sake tabbatar wa da ’yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin ababen more rayuwa domin samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
A nasa jawabin, Ministan FCT, Nyesom Wike, ya bayyana cewa an bayar da kwangilar aikin ne a watan Oktoban 2025, kuma an kammala shi cikin lokacin da aka tsara.
Ya kuma bayyana cewa kusan kashi 80 cikin 100 na ayyukan da aka kammala a Abuja a halin yanzu, gwamnatocin baya ne suka fara su, yana mai cewa ci gaba da ayyukan da aka gada wata muhimmiyar alama ce ta shugabanci nagari.
Wike ya yabawa Shugaba Tinubu bisa dagewarsa wajen tabbatar da cewa an kammala dukkan ayyukan da aka gada tare da sababbin ayyukan da gwamnatinsa ta ƙaddamar.
Ita ma Ministar Jiha ta FCT, Dr. Mariya Mahmoud, ta bayyana aikin OSEɗ a matsayin wani babban ci gaba a shirin sauya fasalin Abuja, tana mai cewa sabon titin zai taimaka wajen inganta zirga-zirga, bunƙasa sabbin yankuna da kuma ƙarfafa hanyoyin sufuri a babban birnin tarayya.
Ta ce wannan na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na inganta rayuwar jama’a ta hanyar samar da ingantattun ababen more rayuwa.
