Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Ambasada Abubakar Mai Tantan ya bayyana cewa haƙuri da juriya na daga cikin manyan hanyoyin samun nasara a dukkan ɓangarorin rayuwa.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya ce nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben shekarar 2023 da kuma ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa a yau na nuna muhimmancin hakuri da jajircewa wajen cimma buri.
Ya ce al’ummar Kano na ci gaba da amfana da ayyukan gwamnati da suka hada da gina tituna, samar da ababen more rayuwa da kuma haskaka birane da kauyuka.
Mai Tantan ya kuma yi kira ga gwamnoni a fadin kasar nan da su yi koyi da irin wadannan ayyukan ci gaba domin inganta rayuwar al’umma.
Haka kuma, ya bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta duba yiwuwar rage wasu haraji da ke kara tsadar rayuwa da farashin kayayyaki ga jama’a da ’yan kasuwa.
Ya ƙara da cewa samar da ayyukan yi da bunkasa harkokin kasuwanci na daga cikin hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’umma.
