Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Oluchi Ugbowan, bayan bincike ya gano cewa ita ce ta shirya satar kanta tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 50.
Lamarin ya jawo cece-kuce bayan ’yarta, wacce aka bayyana da suna Majesty Bundle, ta sanar a shafinta na Instagram cewa an yi garkuwa da mahaifiyarta yayin da take kan hanyarta ta zuwa shago. Ta kuma roƙi ’yan Nijeriya masu hali da su taimaka da kuɗi domin ceto ta.
A cewarta a lokacin, wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar tata sun nemi a biya su Naira miliyan 50 kafin su sake ta.
Sai dai mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, CSP Eno Ikoedem, ta bayyana cewa binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya gano cewa matar ce ta ƙirƙiri labarin satar kanta a yankin Ikpoba Hill na jihar.
Ta ce jami’an ’yan sanda sun bi sawun matar har zuwa Jihar Delta, inda suka kama ta a wani otal tare da wasu da ake zargin abokan haɗin gwiwarta ne.
“An gano Oluchi Ugbowan a Jihar Delta, inda aka kama ta a wani otal. Mun kuma cafke dukkan waɗanda suka shiga cikin wannan shiri. Dukkansu sun amsa laifinsu, sannan an ƙwato bindigogin da aka nuna a bidiyon da suka yi amfani da su,” inji kakakin rundunar.
Ta ƙara da cewa za a gurfanar da matar mai shekaru 45 tare da sauran waɗanda aka kama bisa tanadin doka.
Bayan gaskiyar lamarin ta bayyana, ’yar matar ta fitar da wani bidiyo inda ta nemi afuwar dukkan ’yan Nijeriya, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawar kuɗi domin taimakawa wajen kuɓutar da mahaifiyarta.
Ta bayyana cewa abin ya girgiza iyalansu matuƙa, domin ba su da masaniya cewa mahaifiyar tasu ce ta shirya komai.
“Mahaifiyata ta samu ’yanci. Ana gudanar da bincike kuma an gano cewa tana da hannu a lamarin. Gaskiya iyali sun shiga ruɗani. Ni dai na yi abin da kowace diya za ta yi domin kare rayuwar mahaifiyarta,” inji ta.
Ta kuma bayyana damuwarta kan yadda lamarin zai shafi mahaifinta, wanda ta ce yana fama da matsalolin lafiya.
Majesty Bundle ta sanar da cewa iyalansu sun fara mayar da duk kuɗaɗen da jama’a suka bayar domin taimakawa wajen kuɓutar da mahaifiyarta.
Ta buƙaci duk wanda ya bayar da gudunmawa ya tuntuɓe ta tare da hujjar biyan kuɗinsa domin a mayar masa da kuɗinsa.
“Ba ni da hannu a wannan lamari, kuma ba ni da niyyar cutar da kowa. Mun fara mayar da kuɗaɗen ga duk wanda ya bayar. Haka nan muna aiki domin mayar da kuɗaɗen da aka tara ta hanyar GoFundMe ga masu su,” inji ta.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen neman tallafi, tare da nuna muhimmancin bincike da tabbatar da sahihancin bayanai kafin bayar da gudunmawa.
