Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fitaccen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya zama abin tattaunawa a kafafen sada zumunta bayan ya bayyana aniyarsa ta zuba jari a Matatar Mai ta Dangote.
Davido ya wallafa wani saƙo a shafinsa na ɗ (tsohon Twitter), inda ya nuna abin da ake zargin takardar neman shiga wani tsarin saka hannun jari ne a Matatar Dangote. Rahotanni sun nuna cewa an buɗe damar neman wannan jarin ne a ranar 1 ga Yunin 2026, kuma za a rufe ta a ranar Laraba, 10 ga Yuni, 2026.
Matakin na Davido ya zo ne kwanaki kaɗan bayan hamshaƙin attajirin nan kuma mai zuba jari, Femi Otedola, ya sanar da shirinsa na saka dala miliyan 100, kwatankwacin kusan naira biliyan 130, a Matatar Dangote ta hanyar wani tsarin saka hannun jari na musamman kafin kamfanin ya shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari (IPO).
A cikin saƙon da ya wallafa, Davido ya bayyana cewa yana alfahari da kansa saboda wannan yunƙuri, inda ya rubuta: “Ina daf da saka jari a matatar mai ta uban gidana… Ina matuƙar alfahari da kaina.”
Wannan sanarwa ta jawo martani mabambanta daga masu amfani da kafafen sada zumunta. Yayin da wasu suka yaba wa mawakin saboda hangen nesansa na kasuwanci, wasu kuwa sun soki matakin nasa na bayyana irin wannan lamari a bainar jama’a.
Wani mai amfani da shafin ɗ mai suna Moses Williams ya yi masa martani da cewa: “Kai fa dole ne sai ka sanar da mu komai? Ba ka da rayuwar sirri ne?”
Sai dai Davido ya mayar da martani kai tsaye, yana mai cewa abin da ya yi ba neman ɗaukar hankali ba ne, illa ƙarfafa gwiwa ga mabiyansa. Ya kuma yi nuni da cewa mutane masu nasara bai kamata su riƙa ɓoye nasarorinsu ba.
A cewarsa, “Wannan ƙarfafa gwiwa ne ga mutane. Talaka da rayuwar sirri kamar abu ɗaya suke.”
Amsar tasa ta ƙara rura wutar muhawara a intanet, inda mutane da dama suka fara tattauna batun bambancin rayuwar sirri da kuma yadda fitattun mutane ke bayyana harkokinsu na kuɗi ga jama’a.
Wasu daga cikin mabiyansa sun goyi bayansa, suna cewa ya dace attajirai da masu nasara su riƙa nuna irin ci gaban da suke samu domin zaburar da matasa. Sai dai wasu sun dage cewa ba lallai ba ne a bayyana duk wani mataki na zuba jari ko harkokin kuɗi a fili.
Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-cen, lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan tasirin fitattun mutane wajen sauya tunanin mabiyansu game da saka hannun jari da harkokin kasuwanci.
