Ɗan majalisar wakilai Yaya Bauchi Tongo ya rasu

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe

Al’ummar Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya sun shiga jimami bayan rasuwar ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye, Hon. Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu a ranar Juma’a a Abuja bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Marigayin Yaya Bauchi Tongo, wanda ya kasance jigo a jam’iyyar APC kuma fitaccen ɗan siyasa, ya yi fice wajen wakiltar al’ummarsa tare da gudanar da ayyukan ci gaba da tallafa wa mabuƙata a mazaɓarsa da sauran sassan Jihar Gombe.

Rasuwarsa ta zo ne ƙasa da makwanni biyu bayan da jita-jitar mutuwarsa ta yaɗu a kafafen sada zumunta, lamarin da iyalansa, makusantansa da magoya bayansa suka musanta a wancan lokaci.

Da yake bayyana alhininsa kan wannan rashi, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce mutuwar Hon. Yaya Bauchi Tongo babban rashi ne ga Jihar Gombe da kuma Nijeriya baki ɗaya.

A cikin saƙon ta’aziyyar da darakta janar na harkokin yaɗa labarai na gidan gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen ɗan siyasa, ƙwararren ma’aikacin gwamnati kuma wakili mai kishin al’ummarsa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima.

Ya ce gudunmawar da marigayin ya bayar ba ta tsaya a mazaɓarsa kaɗai ba, domin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ci gaban jihar ta hanyar ayyukan raya ƙasa da kuma taimakon jin ƙai ga mabuƙata.

Gwamna Inuwa ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye, Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, mambobin majalisar tarayya, abokan siyasarsa da ɗaukacin al’ummar Jihar Gombe.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi a aljannatul firdausi, tare da bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a sanar da cikakken bayani kan yadda za a gudanar da jana’izar marigayin ba.

By ukarofi