Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnan Jihar Katsina , Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga jami’an gwamnati, masu hannu da shuni da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa ƙarfi wajen yaƙi da cutar ciwon daji, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwa ne kaɗai zai tabbatar da gano cutar da wuri, samar da ingantaccen magani da riga kafi da kuma ƙarfafa harkokin kiwon lafiya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen liyafar bankwana da aka shirya domin karrama tawagar likitocin Revive Mission Belgium da kuma gidauniyar Pledging Aid Charity Foundation (PAC-F) bayan kammala aikin bayar da ayyukan bincike da tiyatar cutar wanda aka gudanar kyauta a jihar.
Gwamna Raɗɗa ya yaba wa tawagar likitocin, PAC-F, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina da ma’aikatan lafiya bisa nasarar shirin, inda ya bayyana cewa ya ƙara bunƙasa wayar da kan al’umma, binciken gano cutar da wuri da kuma ba da magani ga mata. Ya kuma ƙara tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da ƙarfafa wannan haɗin gwiwar a nan gaba.
Tun da farko, shugabar gidauniyar PAC-F, kuma matar gwamnan, Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa, ta bayyana cewa wannan shiri shi ne mataki na farko na yarjejeniyar haɗin gwiwa ta shekaru biyar tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da abokan cigaban ƙasashen daban-daban.
Ta bayyana cewa Jihar Katsina ta zama wuri na uku a duniya, bayan Birtaniya da Belgium, da ta amfana da na’urorin zamani na bincike da maganin cutar daji da aka yi amfani da su a wannan aiki.
Ta ƙara da cewa shirin ya gudanar da bincike ga sama da mata 800, ya yi gwajin kansar mama ga mata sama da 600, tare da gudanar da tiyata 50 da suka ceci rayuka. Ta kuma yi kira ga mata da su riƙa zuwa duba lafiyarsu akai-akai domin gano cutar tun da wuri.
Gidaunyar ta baiwa uwargidan gwamna Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa kyautar yabo kan yadda take aiki tuƙuru wajen yaki da cutar.
