Elon Musk ya zama attajiri na farko a duniya da ya mallaki Dala tiriliyan

Spread the love

Wanda ya samar da kamfanin SpaceX kuma shugabansa, Elon Musk, ya zama mutum na farko a tarihin duniya da dukiyarsa ta haura dala tiriliyan ɗaya, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CNN ta ruwaito.

Wannan nasara ta samu ne sakamakon fara sayar da hannayen jarin kamfanin SpaceX a kasuwar hada-hadar hannayen jari, lamarin da ya jawo gagarumin ƙaruwa a darajar kamfanin.

SpaceX ta fitar da hannayen jarinta kan farashin dala 135 kan kowane kaso, abin da ya sa an kiyasta dukiyar Musk ta haura dala tiriliyan ɗaya.

Hannayen jarin kamfanin, da ake cinikinsu da alamar “SPCX” a kasuwar Nasdaq, sun haura zuwa dala 165 jim kaɗan bayan buɗe kasuwa a ranar Juma’a, wanda ya kai kusan kashi 22 cikin 100 sama da farashin farko na IPO. Hakan ya ɗaga darajar SpaceX zuwa sama da dala tiriliyan biyu.

Kafin fara sayar da hannayen jarin, an kiyasta dukiyar Musk da kusan dala biliyan 813, fiye da ninki biyu na dukiyar mutum na biyu mafi arziki a duniya, wanda shi ne ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Google, Larry Page, mai kimanin dala biliyan 288, a cewar mujallar Forbes.

Yanzu dukiyar Musk ta zarce jimillar dukiyar mutane uku da ke biye da shi a jerin attajiran duniya na Bloomberg, wato Larry Page, Sergey Brin da Larry Ellison.

Da wannan ƙima, SpaceX ta zama kamfani na shida mafi daraja a kasuwar hannayen jari ta Amurka, bayan Nvidia, Alphabet, Apple, Microsoft da Amazon kawai.

SpaceX ita ce uwar kamfanin Starlink, mai samar da intanet ta tauraron dan adam, wanda ke samun riba kuma yana ci gaba da bunƙasa. Haka kuma kamfanin yana da alaƙa da xAI, kamfanin fasahar wucin gadi na Elon Musk da ke gudanar da manhajar tattaunawa ta Grok.

By Babaji