
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce rayuwar marigayi Sarkin Masarautar Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ahmed Ibn Saleh abar koyi ce ga al’umma.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya je jana’iza da ta’aziyyar rasuwar sarkin, wanda ya rasu a ƙasar Misra bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, yana mai cewa wajibi ne ‘yan ƙasa musamman matasa su cigaba da neman ilimi kamar yadda ya wa’azantar.
Da yake ganawa da manema labarai a Damaturu, Jihar Yobe, jim-kaɗan bayan jana’izar marigayin, Shettima ya ce sarkin ginshiƙi ne na haɗin kai, zaman lafiya da son ci-gaban al’umma, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koyi da shi akan haka.
A cewarsa, marigayin ya rayu cikin mutunci da girmamawa musamman ta amfani da matsayinsa wajen kira ga neman ilimin don inganta al’umma da yankunansu.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yi masa addu’ar samun rahamar Allah (SWT), tare da jajenta wa iyalansa bisa rashinsa.
A ƙarshe, ya yi addu’ar fatan samun zaman lafiya da ci-gaba a Nijeriya, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa yi wa jagororinsu addu’a, kamar yadda kakakinsa, Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.


