Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da sabbin matakai da nufin ƙarfafa ɗa’a da gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati a ma’aikatu, sassa da hukumomin tarayya, inda ta ƙayyade iyakar kuɗaɗen gudanarwa da jami’ai za su iya kashewa tare da ƙaƙaba sabbin ƙa’idojin sa ido da bayar da rahotanni.
Sabbin umarnin na ƙunshe ne cikin Takardar Izinin Kuɗaɗen Gudanarwa ta Shekarar 2026, wadda Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya amince da ita, sannan Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar da ita ta wata sanarwar baitulmali.
Takardar, mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Yunin 2026, ta samu sa hannun Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi. Ta ba jami’an lissafi a bangarorin zartarwa, majalisa da shari’a damar amincewa da kuɗaɗen gudanarwa ga waɗanda suka cancanta, tare da shimfiɗa sabbin ƙa’idojin kashe kuɗi da bin doka.
A ƙarƙashin sabon tsarin, ministoci za su iya karɓar kuɗaɗen gudanarwa da ba za su wuce Naira 700,000 ba domin biyan kuɗaɗen ayyukan hukuma da za a mayar musu daga baya.
Babban Sakatare da manyan daraktocin kuwa an ƙayyade musu Naira 500,000, yayin da daraktoci da shugabannin sassa za su iya karɓar har zuwa Naira 300,000.
Haka kuma, shugabannin ofisoshi a jihohi da sauran jami’an da aka ba izinin karɓar irin waɗannan kuɗaɗe ba za su wuce Naira 100,000 ba.
Ofishin Akanta Janar ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Tsarin Kuɗi ta Tarayya (Financial Regulation 1003), kuma wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa gaskiya da kula da dukiyar jama’a yadda ya kamata.
Sanarwar ta ce an bai wa dukkan jami’an lissafi a ma’aikatu, ofisoshin gwamnati da hukumomi ikon amincewa da kuɗaɗen gudanarwa ga waɗanda suka cancanta, amma a cikin iyakokin da aka ƙayyade.
A wani muhimmin mataki na daƙile almubazzaranci da ƙarfafa kula da kashe kuɗi, gwamnatin ta kuma taƙaita yawan lokutan da za a iya mayar wa jami’ai kuɗaɗen gudanarwar da suka kashe.
Sabuwar dokar ta tanadi cewa a al’ada, za a mayar da irin waɗannan kuɗaɗe sau ɗaya ne kawai a kowane zangon watanni uku. Sai dai idan akwai wata buƙata ta musamman, ba za a amince da mayar da kuɗin fiye da sau biyu cikin zangon watanni uku ba.
An bayyana cewa wannan tsari zai taimaka wajen tilasta tsara kashe kuɗi yadda ya kamata tare da rage yawan neman kuɗaɗen gaba ba tare da wata buƙata ta haƙiƙa ba.
Gwamnatin ta kuma umurci dukkan jami’an lissafi da masu kula da kashe kuɗi da cewa duk wata sayayya ta kaya ko sabis da ta haura Naira miliyan ɗaya dole ne a bi tsarin bayar da kwangila kamar yadda Dokar Saye da Kwangila ta ƙasa ta tanada.
Sanarwar ta ce ba za a yi sayayyar cikin gida da ta zarce Naira miliyan ɗaya kai tsaye ba, sai ta hanyar tsarin kwangila, in banda wuraren da dokar ta ba da wani tanadi na musamman.
An ce matakin zai ƙara tabbatar da gaskiya, adalci da bin doka wajen gudanar da harkokin saye da kwangila a hukumomin gwamnati.
Domin ƙarfafa sa ido da riƙe bayanai, gwamnati ta umurci dukkan ma’aikatu da hukumomin da ke kula da kuɗinsu da kansu da su gabatar da cikakken rahoto ga Ofishin Akanta Janar cikin kwanaki 30.
Rahoton zai ƙunshi bayanan yadda aka rufe asusun kuɗaɗen gudanarwa na shekarar 2025, tare da sunayen jami’an da aka amince musu da kuɗaɗen gudanarwa a shekarar 2026 da wuraren aikinsu.
An bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ƙara sa ido kan yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati.
Sabon tsarin ya kuma wajabta wa duk masu karɓar kuɗaɗen gudanarwa buɗe asusun banki na musamman domin gudanar da irin waɗannan kuɗaɗe, daidai da manufar gwamnatin tarayya ta amfani da tsarin biyan kuɗi ta yanar gizo.
Za a riƙa gabatar da rahoton wata-wata ga Ofishin Akanta Janar, wanda zai nuna kuɗaɗen da aka tura cikin asusun da kuma takardun da ke tabbatar da yadda aka kashe su.
Wannan mataki na daga cikin yunƙurin gwamnati na rage amfani da kuɗi a hannu da kuma ƙara amfani da tsarin zamani wajen sarrafa kuɗaɗen gwamnati.
