Bauchi da Gombe sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da NNPC su duƙufa haƙo man fetur a jihohin

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Maƙotan jihohin nan na Bauchi da Gombe da ke shiyyar Arewa maso gabashin Nijeriya sun haɗa bakunansu suna masu kira wa Gwamnatin Tarayya da ta yi wa Allah da Annabin Sa, ta shawo kan Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) domin ya duƙufa tono ɗimbin man fetur da na gas da ke danƙare a sassan jihohin su.

Man fetur da na gas dai, waɗanda aka gano a sassa da gangajiyar abokan jihohin biyu a lokatai masu tsawo da suka gabata, kuma Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya tabbatar da ɗimbin yawan su a kwazazzaban Kolmani na ƙauyen Barambu, da suka kai kimanin yin kasuwanci, amma NNPC ta yi watsi da su lokaci mai tsawo, ba as balle cas.

Shugabannin Ƙungiyoyin Ƙananan Hukumomi (ALGON) na jihohin Bauchi da Gombe, Hon. Yusuf Garba Alkaleri da Barista Abdulahi Mohammed Inuwa sune suka yi wannan matashiyar a wata ganawa da suka yi da manema labarai a birnin Bauchi, a kwanakin baya.

Hon. Yusuf Alkaleri ya bayyana cewar, haƙo man fetur da na gas a jihar Bauchi, husasan ma a cikin ƙaramar hukumar sa ta Alkaleri, za su bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan, kana su samar wa matasa da ke karkara, da ɗaukacin shiyyar Arewa maso gabas xiimbin ayyukan yi a tsakanin su.

Alkaleri ya yi la’akari da cewar, duƙufa ga haƙo man zai sanya jihohin biyu shiga cikin tawagar jihohi masu tutiya da samar da man fetur a ƙasar nan, sai ya ƙara da “kan gano man fetur da na gas a kwazazzabun Gongola da kwatarniyar Benuwai, muna godiya wa Allah da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa goyon baya na samuwar su a yankin.

“Muna neman goyon bayan Gwamnatin Tarayya domin sanya ƙaimi wa kamfanin man fetur na ƙasa ya himmatu ga yin gamajigon man fetur da na gas da yake ajiye a jihar Bauchi domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, da na jama’a,” a cewar shugaban na ALGON.

Hon. Yusuf Alkaleri ya lura da cewar, duk da buƙatar bin wasu zayyanannun ƙa’idoji, lamarin zai yi tagomashi idan gwamnatin  tarayya za ta himmatu wajen ɗebo ɗimbin man fetur dana gas da suke shimfiɗe, kuma yawan su ya kai ga yin kasuwancin su a yankin na ƙauyen Barambu ta cikin ƙaramar hukumar Alkaleri.

Alkaleri ya yaba wa Kamfanin Mai na NNPC bisa ƙoƙarin ta na biyan diyya wa masu gonaki da haƙo man a yankin ya shafa, yana mai cewar, “muna buƙatar sayar da albarkatun mai domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, da kuma samar da ayyukan yi wa ɗimbin masu zaman kashe wando.”

Yusuf, sai ya nuna godiyar sa wa gwamnan jiha, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed bisa ƙoƙarin sa na samar da kyakkyawan yanayi da abubuwan more rayuwa kamar makarantu, asibitoci da wasu kayayyakin alatu na gudanar da haƙon mai hankali a kwance.

Da yake tofa albarkacin bakin sa, shugaban ƙungiyar ƙananan hukumomi a jihar Gombe, Barista Abdullahi Mohammed Inuwa ya bayyana cewar, rijiyoyin man fetur guda uku aka gano a yankunan na jihohin Bauchi da Gombe, sai ya yi kiran a gaggauta haƙo man na fetur domin bunƙasa tattalin arziki.

Inuwa a furucin nasa ya ce, “rijiyoyin mai guda uku aka gano a yankin. Muna matuƙar buƙatar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya su gina ƙananan matatun mai a yankin, da kuma kai man kasuwa domin samar da masu gidan rana.”

Ya kuma yi kira ga Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da ya gaggauta biyan diyya wa masu gonakai a jihar Gombe waɗanda ayyukan samar da man suka shafa, yana mai cewar, wasu gonakin cikin jihar da amfanin da ke cikin su duka motocin ayyuka sun murƙushe su.