
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta sanar da rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), wanda ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga bayan garkuwa da shi, tana mai bayyana hakan a matsayin babban rashi ga dakarun tsaron Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Jekdikwatar, Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar a ranar Juma’a, rundunar sojin ta jajenta wa iyalan marigayin, abokan aiki da al’ummar Nijeriya.
A cewar sanarwar, marigayi Manjo-Janar Rabe ya yi wa ƙasar hidima a matakai daban-daban ciki har da riƙe muƙamin kakakin rundunonin sojoji daban-daban da kuma daraktan yaɗa labarai na DHQ, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana ayyuka da tsare-tsaren sojoji ga al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tsohon sojan ya bayar da gagarumar gudunmawa a ƙoƙarin Nijeriya na daƙile ayyukan tayar da ƙayar baya da ci-gaban ƙwarewar aikin dakarun tsaro.
Ta bayyana cewa, ƙoƙarinsa wajen sauka nauyin aikin da aka ɗora masa da haɗin kai a Nijeriya zai zama abin koyi ga jami’an tsaron Nijeriya.
A saboda haka ne dakarun tsaro suke hoɓɓasa wajen faɗa da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da wasu nau’ukan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
An sace Manjo-Janar Rabe ne tare da matarsa, Hajiya Amina Abubakar a yankin .Musawa zuwa Kafin-Soli na Ƙaramar Hukumar Matazu a Jihar Katsina
