Tsadar fetur: ActionAid ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan gaggawa domin ceton ’yan Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Kungiyar agaji ta ActionAid ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan taimakon tattalin arziki na gaggawa, sakamakon yadda rikicin duniya da ya shafi ƙasashen Iran, Isra’ila da kuma Amurka ke ƙara tsananta matsin rayuwa ga al’ummar Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Abuja ranar Lahadi, ta bayyana cewa rikicin da ya shafe sama da wata guda yana haifar da hauhawar farashin mai, kuɗin sufuri da kuma kayan abinci, lamarin da ke ƙara jefa miliyoyin ’yan Nijeriya cikin talauci.

ƙungiyar ta nuna damuwa kan rashin wani tsari mai ƙarfi da haɗin kai daga Gwamnatin Tarayya wajen rage tasirin girgizar tattalin arzikin makamashi da duniya ke fuskanta.

A cewarta, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi daga kusan dala 75 zuwa 80 a kowanne ganga kafin rikicin zuwa kusan dala 100, sakamakon tangarɗar samar da mai daga yankin Gabas ta Tsakiya. Duk da haka, ƙungiyar ta ce ya kamata Nijeriya ta ci gajiyar wannan ƙaruwa, duba da yawan ɗanyen man da take fitarwa.

Ta bayyana cewa Nijeriya na samar da tsakanin ganga miliyan 1.3 zuwa 1.5 na ɗanyen mai a kullum, wanda ke nufin samun ƙarin kuɗaɗen shiga, amma duk da haka, wannan bai kai ga rage wa talakawa wahala ba.

A halin yanzu, ƙungiyar ta ce ana sayar da man fetur tsakanin N1,200 zuwa N1,400 a lita a sassa daban-daban na ƙasar, yayin da dizal ke ci gaba da tsada, abin da ke shafar kusan dukkan fannoni na tattalin arziki.

Daraktan ƙungiyar a Nijeriya, Andrew Mamedu, ya ce halin da ’yan Nijeriya ke ciki yana nuna haɗuwar matsalolin duniya da kuma gazawar manufofin cikin gida.

Ya ce, “Ba daidai ba ne a ce ƙasar da ke da arzikin mai kamar Nijeriya ba ta iya kare al’ummarta daga illar tashin farashin mai a duniya ba.”

Ya ƙara da cewa wasu ƙasashe sun riga sun ɗauki matakan kariya, inda ya kawo misalan ƙasashen Thailand da Indonesia, waɗanda suka aiwatar da shirye-shiryen tallafi da rage farashi domin kare jama’arsu.

Binciken da ƙungiyar ta gudanar a matakin al’umma ya nuna cewa gidaje da dama sun fara ɗaukar matakan ƙunci, kamar rage yawan cin abinci, cire yara daga makaranta saboda kuɗin sufuri, da kuma karɓar bashi domin rayuwa.

Haka kuma, ƙananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu na raguwa ko ma rufewa gaba ɗaya saboda tsadar dizal da jigilar kaya, yayin da ma’aikata na yau da kullum ke fuskantar raguwar kuɗin shiga.

Domin magance matsalar, ActionAid ta buƙaci Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar jihohi da ƙananan hukumomi da su aiwatar da tsari na gaggawa da ya haɗa da bayar da tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi, dawo da tallafin mai na wucin gadi, da kuma rage wasu haraji da ke ƙara tsadar mai.

Ta kuma ba da shawarar ƙarfafa tsarin “ɗanyen mai da naira”, tallafa wa tsarin sufuri na jama’a, da kuma kare harkokin rabon abinci da kayan kiwon lafiya daga illar tsadar sufuri.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada cewa duk da cewa rikicin duniya na iya kasancewa a wajen ikon Nijeriya, amma matakan da gwamnati za ta ɗauka suna hannunta ne, don haka ya zama wajibi ta gaggauta kare al’ummarta daga ƙarin wahala.

By ukarofi

Leave a Reply