Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da matsalolin tsaro ke ƙara aamari a Nijeriya, ƙungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda ya yi alƙawari.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa Abubakar Jiddere ya sanya wa hannu.

Manyan na Arewa sun ce matsalar tsaro ta kai matsayin da ke buƙatar ɗaukar matakai na gaggawa.

Sanarwar ta ce, idan ba a ɗauki tsauraran matakai ba, akwai yiwuwar ƙasar ta faɗa cikin ruɗani da rashin doka da oda.

ƙungiyar ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya na rayuwa cikin tsoro, al’ummomi na fuskantar hare-hare, yayin da masu aikata laifuka ke aara samun ƙarfin gwiwa.

Sanarwar ta ce: “ƙungiyar Dattawan Arewa ta nuna matuƙar damuwa kan yadda tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a faɗin Tarayyar Nijeriya.”

Ta ƙara da cewa, babu wata ƙasa da za ta yi iƙirarin ci gaba idan mutanenta na rayuwa cikin tsoro, yayin da miliyoyin masu bin doka suke cikin haɗari.

ƙungiyar ta tambayi dalilin da ya sa ‘yan ƙasa ke kare kansu daga masu garkuwa, ‘yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuffuka.

Ta ce, tun bayan samun ‘yancin kai a 1960, Nijeriya ta fuskanci ƙalubalen tsaro iri-iri, amma ba a taba ganin irin wannan ba.

A cewarta, daga Zamfara da Katsina zuwa Kaduna da Neja, daga Filato da Benuwe zuwa Kogi, Kwara, Borno, Oyo, Edo, Enugu da Imo, hare-hare sun zama ruwan dare.

ƙungiyar ta ce ana kai wa al’ummomi farmaki, ana sace mutane, manoma suna barin gonakinsu, yayin da matafiya ke fuskantar hari a manyan hanyoyi.

Ta bayyana cewa rahotannin tsaro masu zaman kansu sun nuna dubban mutane sun mutu ko an sace su sakamakon ayyukan miyagu.

NEF ta ce, matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta rikiɗe zuwa wata babbar kasuwanci ta ta’addanci mai cin gajiyar raunin tsaro.

By ukarofi

Leave a Reply