Mutum ne haziƙI wanda duk wanda ka tambaya shaida a kansa abu biyu yake faɗa na farko, mutum ne mai tsoron Allah sai kuma tausayi. Ya jima yana gwagwarmaya kan tallafawa al’umma da siyasa ba a iya Katsina ba a duk arewacin Nijeriya ba inda ba a ji da ganin tallafin Gwagware foundation ba. Jaridar Manhaja ta tattauna da Dr Dikko Umar Raɗɗa don jin me ne sirrin nasararsa da kuma abin da ya sa a gaba yanzu.
Taƙaitaccen Tarihinka.
Dr Dikko Umar Raɗɗa Gwagwaren Katsina shugaban ƙananan da matsakaitan masana’antu na ƙasa kuma shugaba na Gwagware Foundation wanda wannan gwagware Foundation ɗin wata NGO ce wadda take tallafawa marayu da marassa ƙarfi da gajiyayyu. An haife ni a 1969 a garin Dutsimma a hayin gada. Na yi makarantar firamare a garin Raɗɗa sannan na yi makarantar sakandire a Zariya teachers college sannna na yi makarantar kwalejin horon malamai a Kafancan inda na ƙare a 1984 na sami takardar shaida ta NCE a 1992 na koma jami’a a Abubakar Taɓawa Ɓalewa a Bauchi na sami digiri a B.A na dawo na yi bautar ƙasa a Jos. Bayan na Kammala sai na fara digiri na biyu sannan na kuma yin wani masters ɗin a ɓangaren Agricultural extension and rural sociology. Na kuma yin Masters a international Relationship and Diplomacy a ABU Zaria. Sannan na yi PhD ɗina a Agric Extension and Rural Sociology.
Gwagwarmaya
Na fara da koyarwa inda na jima ina yi, na yi shekara goma ina yi. Sannan na koma banki a shekarar 1991inda anan ma na yi aiki na shekara biyar. Bayan n agama a shekara ta 2003 Maigirma Shugaban Ƙasa marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa yana gwamnan jihar Katsina ya ba ni kantoman riƙo a ƙaramar hukumar Chiranci inda na share kusan shekara ɗaya da rabi ina kan wannan kujera. Bayan an yi zaɓe sai na zama zaɓenɓen ciyaman na wannan ƙaramar hukuma ta Chiranci ƙarƙashin jam’iyyar PDP wanda muka yi har zuwa shekara ta 2008 kuma daga nan na bar shugaban ƙaramar hukuma muka shiga harkar kasuwanci muka kafa kamfanoni muna kasuwanci muna kuma taɓa kasuwanci har lokacin da muka canza muka ƙirƙiro wata ƙungiya a ciki jam’iyyar PDP wadda ake cewa PDP reform forum ƙarƙashin shugabancin Ken Innamani yana Senate President lokacin Alhaji Bello Masari yana Speaker na Nijeriya daga nan muka tsunduma jam’iyyar Janar Muhammadu Buhari a 2011 a jam’iyyar CPC inda na tsaya takarar ɗanmajalisa kuma ba mu samu nasara ba daga nan na zo na riƙe muƙamin Senior Legislative Aids na sanata.
Bayan mun gama a 2014 aka zaɓe ni sakatare na jam’iyyar APC wanda mu ne National Working Committee na farko waɗanda suke Opposition Party muka kafa gwamnati wadda ta kawo gwamnatin Janar Buhari inda ina National Welfare na APC maigirma gwamnan jihar Katsina ya ba ni Chief of Staff inda na je na yi aiki ƙarƙashin wannan muƙami a ofishin gwamna bayan na yi wata takwas ina wannan aiki sai kuma Allah ya sa Maigirma Shugaban Ƙasa ya ba ni shugbanci na wannan hukuma ta ƙanana da matsakaitan masana’antu a 2016 shi ne muke a kai wanda a wannan watan na Maris da ya wuce na bana wa’adina ya cika a wannan ofishin sannan kuma aka ƙara ba ni dama na na maimaita wannan kujerar na tsahon shekara biyar in Allah ya ba mu yawan rai.
Wanne Aiki ne Gwagware Foundation ta ke yi?
Ita Gwagware Foundation ƙungiya ce wadda muka kafa a shekarar 2015, mun kafa wannan gidauniya ne don mu taimakawa marayu mata gajiyayyu waɗanda mazansu suka mutu ko kuma zaurawa da ‘ya’ya marayu da mata aka bari da marayu da masu nakasa masu larura. Waɗannan su muke gani suna da matsala sai muka gay a kamata mu da Allah ya ba wa dama ya ba mu ilimi ya ba mu sanin rayuwa ta duniya bakin gwargwado kuma ya ba mu abin hannu dai-dai gwargwado muka ga cewa ya kamata mu ma mu yi wani abu da zai taimaka al’ummar domin mu ma wata rana ‘ya’yanmu za su zamo marayu matanmu za su zama iyayen marayu idan ka kalli irin wannan abubuwa sai ka ga ya zama dole ka taimaka su ma waɗannan da suke da wannan matsala ba su suka ƙirƙirawa kansu ba, haka Allah ke san ganinsu don haka ya zama wajibi gare mu, mu da Allah ya ba wa dama don su ma su kai kowanne matsayi.
Kusan san da muka fara abubuwa da dama muka kalla mun buɗe ɓangare biyu akwai Gwagware Foundation Women Empowerment Programme akwai kuma Gwagware Foundation kawai. To shi na farkon muna ba da fifiko ne a wurin mata saboda mata suna da rauni kuma suna da rawar takawa sai kuma ɗayan shi kuma muna koya wa matasa da marayu da waɗanda ba su da galihu sana’o’i kuma muna raka su da jari wanda za su haɓaka kasuwancin wannan jarin da shi za su fara. Daga lokacin da muka fara zuwa yanzu matasan da muka ɗauka muka ba su horo kuma muka ba su jari za su kai 15,000 a jihar Katsina. Wanda mun zagaye jihar Katsina kaf muna wannan tallafin. Sannan haka mun zagaye dukkan ƙananan hukumomin jihar Katsina inda muka ba wa yara tallafin ilmi waɗanda sun gama makaranta sakandire ko ba su ci jarrabawarsu ba, muka ga cewar ya kamata mu jawo su don haka muka sami malamai waɗanda ke koya musu darasi in kuma sun gama darasin sun kware sai mu sake biya musu jarrabawa don su sake zama don gyara takardunsu don wucewa gaba. Sannan saboda ganin muhimmancin ilimin kwamfuta ya sa muka bi zone ɗinmu uku Funtua da Daura da Katsina muka ba wa matasa horo na musamman kan kwamfuta muka kawo wata makaranta kwararriya ta kwamfuta muka yi haɗin gwiwa da su waɗanda ka ba su certificate wanda wannan shaida suna iya aiki da ita a ko’ina.
Sannan mun ware ajin yaƙi da jahilci inda ake koya musu karatu da rubutu da lissafi da ɗinki da saƙa da yin takalma da dai sauran sana’oi na mata da omo da sabulu da man shafawa kuma mu ba su jari. Sannan a ɓangaren marassa lafiya kuma nan ma muna tallafawa dai-dai ikonmu. Sannan a kwanann nan mun kawo wasu likitoci suka zo suka buɗewa makafi idanu suka yi wa marassa lafiya aiki na ciwace-ciwace wanda a wannnan lokacin mutum dubu huɗu suka amfana daga irin wannan tsarin. Duk shekara muna bayar da tallafi ga marayu da gajiyayyu da gidajen marayu muna haɗawa da ƙungiyoyin ɗariƙu da izala muna raba kayan abinci kamar shinkafa da gero waɗanda ake rarrabawa a kowacce ƙaramar hukuma da ke jihar Katsina. Wannan shi ma shekara biyar muna yi, ko wannan azimin da ya wuce mun ƙaddamar da shi.
Sannan muna duba wasu ƙungiyoyi na ƙasashen waje da suke tallafawa kamar abin da ya faru a babbar sallar bana inda muka kawo ƙungiyar Hassene International, wadda ƙungiya ce daga ƙasar Turkiyya wadda take ƙarƙashin jagorancin Shehi Abdul’ahad Sheikh Ibrahim Inyas na Kaulaha. Wanda shekara biyu muna maganar inda suka zo a bana Katsina ƙarƙashin Gwagware Foundation muka zo aka raba wa talakawa shanu ɗari bakwai, wanna gagarumar nasara ce wanda talakawa dubu huɗu da ɗari takwas suka amfana a ranar sallah. Maigirma gwamna ya buɗe. Abubuwan suna da yawa misali lokacin da aka samu matsalar rashin tsaro a jihar Katsina inda aka yi ta samun ‘yan gudun hijira suka cika waɗannan ƙananan hukumomin tara inda suke fama da waɗannan rikicin muka kai musu kayayyakin abinci da kayan sawa da sauran abubuwan masarufi. Duk waɗannan abubuwan a bayyane suke al’umma suna gani kuma muna nan da su a rubuce littafi guda komai na nan.
Me ne Ayyukan Hukumar da ka ke shugabanta a yanzu ta SMEDAN?
SMEDAN hukuma ce wadda take kula da ƙanana da matsakaitan masana’antu hukuma ce da take alaƙa da ba wa masu ƙananan masana’antu dama da haɓaka su da horar da su da ƙirƙiro abubuwa don taimaka musu ta hanyar da za su tallata kayansu sannan mu raine su, mu tallafe su da duk abin da kuke tunani sannan mu bu]e idanunsu akan abin da za su tallafawa sana’oinsu . Semedan ba ta bayar da bashi amma dai tana buɗe ƙofofin samu, muna haɗa su da inda za a sai kayayyakinsu. Misali ko zuwanmu Kano a gobe Opportunity Fair ne wanda za mu zo mu tara mutane masu ƙanana da matsakaitan sana’oi kowa ya tara fasaharsa da ya yi sannan mu kuma mu kira mutane su zo su ga irin basirar da mutanensu suke da ita kuma su zo su sayi abubuwan da suka yi. Irin wannan kiran ne shugaban ƙasa kullum yake yi kan mu riƙa amfani da kayayyakin da muka yi idan mutumin Najeriya bai yi amfani da kayansa na Najeriya ba to wa ka ke tsammani ya zo ya sai naka. Muna da raina abin da muka yi da raina abin da yake namu. Amma yana da muhimmanci ya ma zama dole mu gina sana’oinmu da abin da yake namu domin tallafawa masu yin sana’o’i.
Arewa suna amfana da wannan tsarin naku na SMEDAN?
Arewa suna amfana kwarai da gaske musamman yanzu duk abin da ake yi ana amfani da yanar gizo ne saboda haka za ka ga duk wasu abubuwa da tallafin da gwamnati ke yi sai dai a neme shi ta hanyar internet a da a irin wannnan sai ka ga Arewa na baya amma a yanzu saboda wayar da kan da kullum muke yi sai ki ganmu a kan gaba.Misali a tallafin da gwamnati ta yi na survival fund miliyan dubu saba’in da biyar, za a ga da muka yi shela muka ƙara tallata abin sai ya kasance waɗanda suka zo na farko a cikawa mutanen Kano ne sai jihar Kaduna sai na uku jihar Lagosa sai na huɗu jihar Katsina. Kusan jihohin farko jihohin arewa ne. Wannan ya sa har wasu ke tsogumi ko don muna bisa kujerun ne wanda wannnan ba haka ba ne. Mu ba wani abu muka yi ba kawai mun yi amafani da gidajen radiyon ne wajen wayar da kai da sa su a hanya. Kuma mutane sun amshi kiran za ka je ƙauye ka tatar yaro ya sai data yana abubuwa a waya in ya taimaka ya sai datar a yi ire-iren wannan abubuwan masu amfanarwa sai ka ga komai ya zo da sauƙi. Alhamdilillahi mutanenmu na tasowa suna kuma kai wa inda ake so su kai. Sau tari in kin ga matsala to mu ma da halayyarmu mun cika ragwanci da son bilis da tunanin aikin gwamnati kuma ga shi yanzu aikin gwamnatin babu shi ga miliyoyoin mutane ke kammala karatunsu na gaba da sakandire za ka ga cewa abubuwan sai an bi tsari. Yanzu yaranmu da dama suna ta ƙirƙiro ayyukan dogaro da kai in sun kammala jami’a ba sa ma tsayawa nemnan aikin gwamnati. Abin da muke kira da gwamnati shi ne ta bayar da dama ga wani banki don masu ƙanna da matsakaitan masana’antu ya za a yi a raine su a ba su tallafi in sun kammala jami;oi har a kai ga gaci.
In ana batun magajin Masari ana sa ran kana ciki waɗanda aka hasashe in hakan ta tabbata me ne fatanka ga Katsinawa.
Da farko ina yi wa Allah godiya a ce kaf jihar Katsina amma a ce an yi tunaninka a jerin farko na wanda ake sa ran gadar gwamna wannan ba ƙaramar baiwa ce ba da za a yi wa Allah godiya, ba ƙarfinka ba ne ba iyawarka ba ce ba kuma don ka fi kowa ba ne .Na biyu mu da muke hidimar siyasar nan kusan shekara talatin mun san abin bakin iyaka kuma abin da ake fata shi ne Allah ya ba ma jihar wanda zai taimakawa jihar Katsina da tallafa mata fita daga cikin matsalolin da muke da su a jihar Katsina kuma ni ɗan siyasa ne na daɗe ina siyasar nan wadda ita ta kawo mu inda muke a yau. B azan ce zan yi takarar gwamna ko ba zan yi ba, amma dai ina tabbatar wa jama’a cewa duk wani kira da jamaa za su yi mana domin mu zo mu tallafi jihar Katsina a shirye muke mu amsa kiran kuma shirye muke mu yi. Amma mu abin da muka sani shi ne mulki daga Ubangiji ne shi ne yake bayarwa kuma ba babba ba yaro, ba yawan ilimi ba ne ba yawan shekaru ba ne ba iyawa ba ne ba alaƙa ba ne ku kuɗi ko muƙami ba ne. Allah ya zaɓarwa jihar Katsina shugabanni tiryen-tiryen .Kuma in sha Allahu gwamnan da zai zo 2023 muna yi masa addu’ar ya zama ma fi alheri ga jihar Katsina. Allah ya riga ya san ko wa ye zai yi gwamnan ko ni ina so ko ba na so, ko wani na so ko ba ya so wannan shi ne abin da za mu kalla. Mu fatanmu mai zai taimakawa jihar Katsina. Idan ni ne na fi dacewa kuma zan kawo abin da ake so a yayin gudanar da mulki Allah ya tabbatar in kuma akwai wanda ya fi mu dacewa da alheri kuma shi mutanen Katsina suka ga ya fi dacewa su zaɓa laba’asa, mu abin da muke fata shi ne a ga cewar an samu ingantaccen shugabanci an ssamu ƙasa ta gari an samu ingantattun mutane waɗanda suke cikin gwamnati waɗanda za su kawowa al’umma ci gaba da walwala wanda shi ake fata. Don mu ci gaban al’umma muke fata wadda za a yi alfahari muke so. Mu a yanzu mun wuce a ce muna son mulki don isa ko don jiniya ko don wani abu da za a samu a ƙarƙashin kujerar gwamna shekarunmu sun kai na mu sa hankali da lura kuma mu fahimci cewa mun fara neman wajen da ƙaburburanmu suke wanda ya fara kallon inda ƙabarinsa yake abin duniyar nan ba shi ne a gabansa ba, abin da zai zama a gabanka shi ne in ka rasu ka bar abin da za a kalli ‘ya’yanka a ce “ wannan ‘ya’yan mutumin kirki ne” shi ne bayan da muke son mu bari don babu amfani ka rayu ka bar duniya amma ka bar sunan banza ana la’antar ‘yayanka wannan shi ne a tunanin da ya fi dacewa. Don haka in ni na dace aka zaɓa, za mu yi abin da ya dace, haka in wani ne ma aka ga y a fi dacewa shi ma za mu ba shi duk goyon bayan da ya dace. Don duk abin da za a yi in babu haɗin kai to babu nasara sannan ba wanda zai ce zai iya kawo gyara shi kaɗai dole sai an haɗu an yi kama-kama. Dole ka nemo mutane masu tunani irin naka da hangen nesa irin naka domin dai a kama a kai uwa juji.
Ya ka kalli hangen mai girma gwamnan jihar Katsina Rd Hon Aminu Bello Masari kan ba zai ba wa wanda ya ɗara shekara 60 mulkin Katsina ba?
Wannan ko ba maigirma gwamna ba, a wannan yanayin na mulki da muke ciki a wannan yanayin ƙasar da muke ciki mulki ba na mai yawan shekaru ba ne. Dalili kuwa shi ne, ba banza ka ga Bature ya ce in ka shekara sittin ka ajiye aiki ba, ka yi ritaya saboda duk lokacin da ka kai wannan shekarun kamai naka ya fara rauni. Idan ƙarfi da abubuwa na rage maka to kuma ai bai dace ka tunkari aikin ƙarfi ba, bai kamata ka tunkari aikin da ke buƙatar tunani ba, aikin da yana buƙatar lafiya cikakkiya da tunani ingantacce, yana buƙatar ƙarfin lafiyar jiki da za a zagaya, ba wai ka zama gwamna ba ne ka zauna a ofis ba. Gwamnati da mulki ya wuce a ce je ka yi kaza dole a je a gani. Misali je ka kalli Maiduguri kaɗai ya ishe ka isharar cewa daya kai waɗannan shekarun ba za ka gan shi ko’ina ya je ya yi tsalle nan ya h au can ya ruga a guje can. Kuma duk yadda ka so je ka yi ba ta yi sai ka je ka gani. Anan ƙasar ne za ka ga irin waɗannan amma ga ƙasashe nan irin su Amurka su Faransa shugabaninsu shekarunsu nawa? Amma dai mutane suna da zaɓi amma abubuwa na gaskiya dole a faɗe su. Ko mu ɗin nan zuwa wani lokacin za mu kauce mu bar wa ‘yan baya su taso. Ko a ƙasar nan a baya in mun kalla akwai lokacin da ‘yan shekara ishin da ‘yan kai ne suka riƙa yin ministoci . Amma a yau muna yanayin da za a ga ɗan shekara tamanin yana minister ana meeting yana gyangyaɗi.
Ya ka ke ganin Shekaru Shidan Gwamnan Katsina Rt Hon Bello Masari a mulkin jihar Katsina?
Shi mai girma gwamnan jihar Katsina Rt Hon Masari mutum ne mai kishin al’umma mutum ne wanda yake da tausayi da hangen nesa mutum ne wanda kullum tunaninsa ya za a yi talaka ya ci gaba kuma ni na yi aiki da shi akan al’amuran siyasa har tsohon shekara goma sha shida mutum ne wanda in ka matse shi za ka tarar mutum ne na kwarai ba ya da baƙin ciki da hassada. Matsaloli da suka dabaibayen jihar guda biyu abubuwa ne da suka addabi ƙasa baki ɗaya ko ma duniya wanda matsaloli ne na zamani. Matsalar tsaro ba Katsina kaɗai ba sun zo daga wurare da dama kuma abu ne da ya daɗe cikin al’umma sai a hankula aka fahimta ya bayyana kuma da ƙarfi sannan a matsalar gwamnonin ta sha kansu ba su da abun yi a kai yadda ya kamata don ya sha kanta sannan mun zo a wannan lokacin tattalin arziƙi ya shiga taɓarɓarewa sau biyu na farko muka fita na biyun ma ya zo muka fita. Za ka ga cewa kafin wannan lokacin a gwamnatin baya lokacin PDP suna samun kuɗin mai ganga daga Dala ɗari ɗaya zuwa ɗari da arba’in amma lokacin da muka hau mulki sai da ta koma dala ishirin da bakwai dala talatin da biyar da tsahon lokaci. Za a ga cewa kame-kame ake. Misali lokacin ina chief of staff za ka ga sai gwamnatin jiha ta cikawa ƙananan hukumomi miliyan ɗari biyu zuwa ɗari uku sannan suke iya yin albashi. Fitintinu ne iri-iri ga matsalar tsaro ga tattalin arziƙi ga matsalar al’umma na talauci wanda suke son a kawo wa rayuwarsu ɗauki ga rayuwarsu. Wannan shi ne abin da ya ɗan dabaibaye gwamnatin amma Alhamdlillah mai girma gwamnan jihar Katsina ya kawo ci gaba sosai a jihar, fatanmu Allah ya ba wa jihar Katsina wanda zai dasa daga inda gwamnan jihar Katsina na yanzu ya tsaya.
Fatanka ga jihar Katsina.
Fatanmu a jihar Katsina shi ne ya ba wa jihar ango na kwarai a shekar 2023 wanda yake da kishin al’umma wanda yake da tsoron Allah wanda yake tunanin talaka ba wanda yake tunanin mai shi ba.
Amin.
Mun gode.