Bidiyo: Tawagar farko ta maniyyata Umura daga Nijeriya ta isa Saudiyya

A yau Asabar tawagar farko ta maniyyata Umura daga Nijeriya ta isa Ƙasar Saudiyya don gabatar da ibadar Umura.

Tawagar ta samu tarba mai kyau bayan da ta sauka a babban filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da ke Jedda a Saudiyya.

Daga cikin jami’an da suka tarbi tawagar har da wakilan Ma’aikatar Hajji da Umura na Saudiyya, ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya, manyan jami’an kula da shige da fice na Saudiyya da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *