Rikicin Filato: Sojoji sun damƙe mutum 12

An samu aukuwar rikici a safiyar Asabar a yankin hanyar Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu.

Bayanan da MANHAJA ta kalato daga yankin sun nuna hatta wasu matafiya da ke wucewa a daidai lokacin da rikicin ya faru, an ƙona musu mota, amma lamarin ya tsagaita sakamakon bayyanar jami’an tsaro a yankin.

Jami’i mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven, Major Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Tare da cewa jami’an rubdunar ta musamman sun bayyana a inda aka samu hatsaniyar bayan da suka samu kiraye-kiraye kan cewa tsegeru sun tare hanya tare far wa mutane.

Ya ce an samu hasarar rayuka yayin rikicin, sannan an kwashi waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don kulawa da su.

Haka nan, ya ce sun sanya ido sosai a kan lamarin, kuma tuni har an damƙe wasu mutum 12 da ake zargi suna da hannu a rikicin inda ake ci gaba da yin bincike a kansu.

A nasa ɓangaren, Kwamandan Rundunar Operation Safe Haven, Major General Ibrahim Ali, kira ya yi ga jama’ar yankin da su taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanan da za su taimaka wajen kamo waɗanda suka haddasa wutar rikicin suka tsere.

Kazalika, ya buƙaci jama’a da a kwantar da hankula a zauna lafiya tare kiyaye dokoki, sannan kowa ya ci gaba da harkokinsa ba tare da wani tsoro ba.

Shi kuwa Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya gargaɗi masu tada zaune tsaye a jihar da su shiga taitayinsu saboda a cewarsa, gwamnati ba za ta lamunci duk abin da zai hana zaman lafiya a jihar ba.