Sarkin Musulmi ga likitoci: Ku janye yajin aiki don amfanin al’umma

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙolin Harkokin Musulunci a Nijeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya shawarci likitocin da ke yajin aiki da su janye yajin aikin nasu don amfanin al’ummar ƙasa.

Haka nan, Sarkin ya roƙi likitocin da su yi wa Allah, su dubi halin da ake ciki na fama da annobar korona da kuma ɓarkewar cutar amai da gudawa a wasu sassan ƙasa, sannan su dakatar da yajin aikin nasu.

Sarkin ya yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Malam Zubairu Usman-Ugwu, ranar Asabar a Abuja.

Sanarwar ta nuna yadda Basaraken ya nuna damuwarsa dangane da yajin aikin da likitocin ƙasar nan suka tsumduma wanda hakan ke ƙara danne marasa ƙarfi a cikin ƙasa.

Sanarwar ta ce, NSCIA ta hararo cewa yajin aikin, ba fannin lafiya kaɗai zai yi wa tasiri ba, har ma da saɓa wa rantsuwar aikin da mambobin Ƙungiyar Likitocin suka sha.

Sarkin Musulmi ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dubi lamarin da idon rahma tare da ci gaba da tattaunawa da likitocin don samun maslaha.