‘Yan bindiga sun sace ɗan gidan hadimin Shugaba Buhari, Abubakar Maikano a Kaduna

‘Yan bindiga sun sace Sanusi Abubakar Maikano, ɗan gidan Alhaji Abubakar Maikano, wanda babban jami’i ne daga cikin hadiman Shugaban Ƙasa Muhammadu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Wannan na faruwa ne bayan da ɓarayi suka fasa gidan Maikano da ke Fadar Shugaban Ƙasa watanni huɗu da suka gabata.

Bayanan jami’an tsaro a Kaduna sun nuna an sace Sanusi ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar Asabar da ta gabata bayan da ya dawo daga gidan gonarsa.

Yayin da wasu shaidu suka nuna an sace Sanusi ne a gidansa da ke Gwantu, hedikwatar ƙaramar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

Da alama dai ‘yan bindigar sun bibiyi Sanusi daga gidan gonarsa har zuwa gida inda suka yi garkuwa da shi kamar yadda bayanan jami’an tsaron suka nuna.

An ce baya ga sace Sanusi da suka yi, ‘yan bindigar ba su cutar da kowa ba a gidan duk da matan Sanusi su biyu a nan gidan suke da zama.

A cewar wata majiya, “Da ɓarayin suka shigo gidan, sun tarar da wasu matasa su uku, ciki har da ƙanin Sanusi. Suka yi tambaya ina Sanusi? Nan aka faɗa musu cewa Sanusi ba ya nan, amma suka nace kan cewa sun ga lokacin da ya sauka a motarsa ba da daɗewa ba.”

A ƙarshe dai ƙaddara ta rutsa da Sanusi inda ‘yan bindigar suka same shi suka yi awon gaba da shi.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani kan wannan lamari daga wajen ‘yan sandan Kaduna.