Shaye-shaye: Ya dace gwamnati ta tallafa wa ƙungiyoyi – Abdulrazaq Shehu

Daga AMINU AMANAWA a a Sakkwato

Idan da akwai wata matsala da a yanzu ta fi damun iyaye da dama, musamman a jihohin Arewa bai wuce matsalar fatauci ko tu’ammali da miyagun ƙwayoyi ba musamman a tsakanin matasa da kuma mata.

Malam Abdulrazak Shehu sanannen mai fafutikar yaqi da matsalar ne musamman a jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara, wanda ma har ya samar da qungiya sukutum domin yaƙi da matsalar wato “Center for Sensitization Against Drug Abuse” a turance.
A zantawarsa da wakilinmu na Sakkwato Aminu Amanawa ya tattauna da Malam Abdulrazak Shehu wanda ya yi bayani sosai kan matsalar da matakan da rawar da ya dace kowa ya taka domin kawar da matsalar a cikin al’umma. Ga yadda zantawarsu ta kasance:

Ka gabatar wa masu karatu da kanka?

Sunana Abdulrazak Shehu, ni ne shugaban ƙungiyar faɗakarwa akan illolin shaye-shaye da ke nan jihar Sakkwato, ƙungiya mai zaman kanta.

Lamarin shaye-shaye za mu iya cewa, abin ƙaruwa yake yi a Sakkwato ko raguwa?

To, matsalar shan miyagun ƙwayoyi da matsalar shan magani ba bisa ƙa’ida ba, lamari ne da ya zamo ruwan dare game duniya, duk duniya tana fama da matsalar shaye-shaye ba Nijeriya kaɗai ba, ko kuma Jihar Sakkwato, duk duniya ne.

A jihar Sakkwato kamar yadda kowa ya sani, jiha ce ta addini don haka kullum malaman addini da limammai kullum aikinsu tsawatarwa, shekaru da dama ansan cewa jihar Sakkwato ita ce cibiyar addini ita a cibiya ta daular Usmaniyya kuma ta yi fice wajen tarbiyya.

To amma yanzu magana ta gaskiya saboda lokaci na canzawa saboda matsaloli da yawa, shaye-shayen nan ya kawo garemu da muna jin wasu ƙasashen, Turai irinsu Amurka, sai ga shi yau dai da yake duniyar ta zamo gari guda, al’adu sun cakuɗe matsalolin sun kawo garemu, kamar yadda ko wanne gari ake yin shaye-shaye Sakkwato ma ana yi, magana ta gaskiya, ana ƙoƙari gefen ita hukumar NDLEA, ana ƙoƙari a gefen ƙungiyoyi irin namu masu zaman kansu, malamai da kowa na yi, don haka wasu na bari wasu na shigowa, don haka matsalar kullum akwai ta ana kanta kuma ana kokari, saboda haka akwai abubuwa da da ake iya la’akari da su wurin ganin abin ya rage, saboda haka kamar ko wacce shekara ya kamata abi diddigi domin a gano, kamar irin wannan matsalar a bayyane ta ke akwai ta magana ta gaskiya ba maganar da ta shafi ra’ayi ba ko kabilarka zaka yi ko ma su addini ka za ke yi, ko masu siyasa kala ka za ke yi, a’a matsala ce wacce akwai ta duk duniya, Nineriya mu ma nan jihar Sakkwato akwai ta tana nan ana ganinta, masu ƙoƙari suna yi gwargwadon iyawarsu, amma tabbas akwaita.

Ban sani ba galibi masu shaye-shayen nan, idan ana tattaunawa da su sukan ce yanayin rayuwa ne ya jefasu ciki, ko kuma da dama daga ‘yan Nijeriya suna ƙorafin yanayi na rayuwa, a iya cewa wannan lokacin buƙatar ƙaruwa ta yi na masu shaye-shayen nan ko raguwa? 

To, ita kamar yadda ka ce lokacin nan da ake ciki yanzu ‘yan Nijeriya kowa ya ji a jikinsa, to amma ita gwamnati kullum tana cewa al’amarin ya taho za a yi ƙoƙari aga abinda za a iya yi, a yi juriya al’amurra za su canja kamar yadda su ke faɗi, to amma magana ta gaskiya rayuwar a halin da ake ciki kowa yasan matsalolin sun ƙaru, tun daga yin ƙarin man fetur kowa yasan abinda ya biyo baya, ita ma wannan magana ce ta gaskiya babu batun addini ko kabila ko na siyasa maganar gaskiya ce, to waɗanda ba su da haquri na juriyar jarabtar ko matsala idan ta taho to sai ka taradda su sun yi abubuwa wa’yanda ba su kamata ba, saboda haka wannan rayuwar da ake ganin Abubuwa sunyi yawa ga al’ummar ƙasa yana yuwa ya zamo hujja ga wasu na su ture su shiga, ko kuma dama suna ciki sai su ci gaba da yi, to amma kullum halin rayuwa idan ya tsananta, wa su suna samun wannan matsalar ta shiga shaye shaye ko sata ko wasu miyagun ayyuka, amma dai ɗan Adam mai hankali idan ya gamu da matsala ta talauci ko wata rashin lafiya ba shi zai sa ya fanɗare ba ko kuma yin abinda bai kamata ba, saboda haka maganar ba zan yi musu ba idan wannan ya zamo wannan Rayuwar da ta tsananta yasa way’ansu su shiga, wanda ko alama ba daidai ba ne.

Ita wannan cibiyar taku ta yi fice a yankin Sakkwato Kebbi Zamfara za a iya cewa ita ce ta farko da ke fafutuka wajen yaƙi da ‘ita wannan matsalar, tun lokacin da aka assasata zuwa yanzu za a iya cewa ta samu nasara dalilin da aka assasata?

Tabbas! To kamar yadda ka ce, wannan yankin namu na Sakkwato Kebbi da Zamfara wannan cibiya ta mu mun fara wannan fafutuka tun shekarar 1997 to asalin ma wannan tun lokacin da muna ɗaliban jami’a ni ne na kafa ƙungiya mai faɗakarwa akan shaye-shaye ta ɗalibai anan Jami’ar Usman danfodiyo wato job free club, Ni na kafata kuma Ni ne shugaba na farko. A wannan lokacin mun gayyato Marigayi Shugaba NDLE Jar Bamai, wannan lokacin ya zauna Sakkwato wurin ƙaddamar da wannan, lokacin shugaban Jami’a wato Sarkin Yawuri na yanzu, Mai martaba Sarkin Yawuri Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi wannan lokacin shi ne shugaban jami’a.

Akwai waɗanda su ka yi ƙoƙari ƙwarai irinsu Farfesa Ƙaura sun taimaka matuka har aka ƙaddamar da wannan block ɗin domin a faɗakar da ɗalibai akan illar shaye-shaye. Sarkin Musulmi na wannan lokacin ya zo da gwamnan jihar Sakkwato anzo an ka yi wannan taron, domin a gwadawa ɗalibai muhimmancin wannan da kuma yaƙi da miyagun ƙwayoyi. To bayan wannan kuma, muna karewa sai muka kawo wannan ƙungiyar, a ƙalla wannan ƙungiyar ta shekara ashirin da uku, har Allah ya kawo mu yanzu tana da wurinta na dindindin! In ka duba manyan ƙungiyoyi ko dai sunyi haya ko Office in ma ƙungiya ta girma kwarai ta ɗauki wani ƙaramin gida a matsayin ko Office ta haɗe.

To Alhamdulillah mu nan da mu ke wurinmu ne na dindindin! Saboda haka munyi shekara ashirin da uku a wannan wurin kuma mafi yawa, duk dai wanda aka ce yana cikin fafutuka na gyara wannan ko gyara wannan ya san muna wannan aikin, mun daɗe muna yi kuma Alhamdulillah, mun yi ayukka da yawa. Taron ƙarawa juna sani mun shiga makarantu muna faɗakar da su kan illolin shaye shaye, mun taimakawa makarantu tun wannan lokacin. Irinsu Sultan Bello, Sultan Attahiru Amadu, da sauran Makarantu. Ka ga na samu sa’a wancan lokacin duk abokanaina ne su ke riƙe da Secondary School, idan muka rubuta takarda sai mu duba wani abokin mu ne, Nagarta College ma, ban mantawa  mun kama, Profesa Abdulkarim tsowon Kwamishina abokina ne na Primary school mun roƙe shi ya zo ya yi lecture.

Mun dai yi abubuwa na faɗakar da al’umma Alhamdulillah. Gidan Rediyo na Sakkwato, NTA Rima Rediyo Vision FM da ta shigo daga baya ma, tun ma way’annan ba su shigo ba, da NTA Sakkwato RIMA RADEO su way’anga mun fi shekara hiye da ashirin muna zuwa program. Muna live program muna recording, kuma ko wacce shekara muna bikin tunawa da ranar ƙwaya ta duniya, 26 Yuni ko wacce shekara majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar yaƙi da miyagun ƙwayoyi na shaye-shaye, ko wacce shekara mu kan shirya lakca domin a tunatar da jama’a a kula.

Daga ƙarshe, wannan tambayar tana da muhimmanci, kowa ka ji shaye-shaye miyagun ƙwayoyi irin da makamantansu ɗin nan, shin ita wannan matsalar akwai matakan sa za’a iya bi ace ta zamo tarihi sai dai ƙila yaran da ke tasowa yanzu a ce da su an yi wata ɗabi’a ta shaye-shaye?

Eh, akwai gaskiya matakan da a ke iya bi ta ragu matuqa, duk duniya ba inda ba a shaye-shaye ashe da ana iya kasheta a kasheta. Miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye sun samo asali ne tun farko. Ka duba Alƙur’ani ya yi maganar giya ko? To Alƙur’ani sadda anka saukar she shi zuwa yanzu shekara dubu da arba’in da huɗu 1444 ana shaye-shaye wannan ya nuna annabawan da su ka zo manzanni gabaninmu, zamanin Annabi Yusufa ana shan giya, to amma yanzu da ya ke duniya ta ƙara yawa, ba wata al’umma da ke da yawa irin ta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.

Don haka wannan matsalar tsohuwar matsala ce to amma dai abinda ya kamata kowa ya yi ƙoƙari ya yi gyara kamar noma ne, a fara da gaba gaba, mu nan jihar Sakkwato duk wanda ke iya taimakawa ya taimaka, ba a cewa NDLEA kaɗai za ta iya wanga aiki, ma’aikata nawa gare mu? Mutum miliyan nawa ke cikin Sakkwato? Gari ɗari nawa ke cikin Sakkwato? Saboda haka Gwamnatin tarayya ta ba su kayan aiki, jihohi da ƙungiyoyi irin na mu duk aci gaba da taimakawa, da ma malaman addini baki ɗaya. Gwamnati ta haɗa kai da ƙungiyoyi ma su zaman kansu a ba su dama su yi faɗakarwa da ya kamata. Idan akwai littafai a bai wa yara da matasa waɗanda ke makaranta da ma waɗanda ba su yi, duk a ba su domin faɗakarwa akai. Malam zaure su shigo ciki a nemi goyon bayansu, idan yau ka sauke Alƙur’ani ka aza Usuluddden ko Ishimawi, ko Ahadhari, da an kammala faɗama karatu sai a kawo illolin shaye shaye.

Limammai a ƙalla ayi huɗuba guda cikin wata bayanin illolin shaye shaye, Malamman ga ma su ɗaukar Loudspeaker suna zuwa wurin ɗaurin aure da wurin zanen suna, suyi ƙoƙari suma a ƙalla ace cikin wata sunyi wa’azi akan illolin shaye shaye ko da sau biyu na wurin ɗaurin aure ko wurin zanen suna, Dattijai su sa baki, Malamman makarantar boko suyi bayani ko da qarshen lecture su wa yara bayanin illolin shaye shaye, in sha Allah idan aka fitowa abin ta ko wanne ɓangare, idan kowa yasa hannu hadda ku y’an jarida dama wannan lokacin na ku ne,  ku ke kai abu ko ina, yanzu wannan firar ta mu, mutum nawa zai ji? Miliyoyi fa, saboda haka ku ci gaba da taimakawa. Ina matuƙar yaba mu ku, ina ga cikin watan ga uku NTA Sakkwato sun zo sun ɗau report, sun zo nan sun yi interview sun je NDLEA, RTV sun zo, yanzu ga ka kai ka zo, watannin baya ma y’an Vision Fm sun gayyace ni, so gaskiya tsakani da Allah ku y’an jarida kun daɗe…

Ni nan da na ke da na ke gayamaka, shekara ashirin da suka wuce ina zuwa NTA da RTV da RIMA RIDEO wurin program, to ka ga duk wannan faɗakarwa ne, idan kunne yaji to gangar jiki ta tsira! To amma matsalolin yanzu gaba ɗaya gasunan, samarin babu harkar yi, shaye shaye sun zamo game gari, matasa sai yawon Office office su ke yi wurin taron siyasa,taron Gwamnati, taron ɗauri aure, taron zanen suna, duk zaka ga matasa ne waɗanda ya dace a ce suna da sana’ar yi ƙasa.

In sha Allah idan aka bi shawarwari za a rage wannan matsalar, babbar matsalar ma sai ka ga yaro ya kai shekara talatin babu karatu babu sana’a, saboda haka ya ka mata asa hannu, y’an siyasa su taimaka su ba da goyon baya su ba da kuɗi ayi abubuwan da ya da ce a ce an taimakawa al’umma, kuma su ji tsoron Allah su bar amfani da su lokacin siyasa wurin kamfen.