Kwanaki 70 ɗaliban Jami’ar Gusau ba su shaƙi iskar ‘yanci ba

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sama da watanni biyu da suka gabata ’yan bindiga da dama sun kai farmaki ƙauyen Gidan Dawa da ke kusa da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da mutum 28, ciki har da ɗalibai mata  na jami’ar, amma har yanzu 12 daga cikinsu su na hannun ’yan ta’addan, sun ƙi sakin su.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau, a wata hira da manema labarai a watan da ya gabata ya tabbatar da cewa, har yanzu ɗalibai 12 na hannun ’yan ta’addar.

A cewarsa, cikin mutane 28 da aka yi garkuwa da su, takwas sun kuɓuta daga hannun ‘yan fashin yayin da sojoji suka kuɓutar da takwas.

A kan ma’aikatan gine-gine guda tara da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su a lokacin harin, Farfesa Mu’azu ya bayyana cewa uku daga cikinsu sun kuɓuta da ƙyar daga hannun ‘yan fashin yayin da sauran shidan ke hannun ‘yan fashin.

Ya kuma tabbatar da cewa, jami’in kula da harkokin jami’ar, Mista Ezekiel Ibrahim, ya na cikin waɗanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su kuma har yanzu su na hannunsu.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin ɗaliban ta mutu a hannun ‘yan bindiga yayin da sauran 12 ɗin ba su san makomarsu ba harya zuwa yau.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 21 ga watan Satumban bana, ‘yan bindigar sun sace mutane 28 ciki har da ɗalibai mata na jami’ar a Gusau babban birnin jihar Zamfara.