’Yan N-Power sun koka da jinkirin biyan alawus da gwamnati ke yi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu dake cikin shirin tallafi na N-Power a ranar Litinin sun koka kan jinkirin rashin biyansu alawus ɗin Naira 30,000 ɗin da gwamnati ke biyansu duk wata.

Masu amfana da shirin sun koka da haka ne ganin yadda suka ɗauki tsawon watanni ba a biya su ba.

Wani Francisco Noah dake cikin shirin Zango C1 ya ce yana koyarwa ne a makarantar makiyaya dake Keffi jihar Nasarawa ya ce rashin biyansu alawus ɗin ya hana shi zuwa wurin aiki.

“Rajistan da na yi na shekara biyu wanda ya kamata a wannan watan Disamban da za mu shiga zai ƙare amma alawus ɗin da na samu na kashe shi ne a watan Nuwamba 2022.

Shi ma Ɗantala dake cikin shirin Zango C2 a fannin harkokin noma ya ce alawus ɗin wata uku ne kaɗai ya samu tun da ya shiga shirin.

“Zuwa yanzu ina bin bashin alawus ɗin wata 9 da ba a biya ni ba.”

Shugaban shirye-shirye na N-Power na Ƙasa Akindele Egbuwalo ya ce gwamnati na ƙoƙarin ganin ta biya masu amfana da shirin alawus ɗinsu.

Egbuwalo ya tabbatar cewa gwamnati ta dakatar da shirin domin gudanar da bincike bayan an gano ƙamiya-miya dake tattare da shirin.

Ya kuma tabbatar cewa gwamnati za ta biya duk alawus ɗin waɗanda suka yi rajistar shirin na gaskiya da zaran ta kammala gudanar da bincike.

By Editor