2027: Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci Obi ya janye daga takara kan iƙirarin bashin Anambara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu a game da rikicin da ke gudana tsakanin tsohon gwamnan Jihar Anambara kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi da kuma gwamnatin jihar bisa bashi da wasu nauye-nauyen da ke kan jihar.

Mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga a wani saƙo ta kafar X a ranar Laraba, ya ce Obi ya yi iƙirarin barin shugabancin jihar Anambara ba tare da wani bashi ba, amma ya yi barazanar cewa zai janye tsaya wa takarar shugaban ƙasa muddin aka tabbatar da wannan iƙirari ba haka yake ba.

Ya bayyana cewa, gwamnatin Anambara ta magantu kan iƙirarin da ya shafi wasu basusuka da gwamnatin tsohon gwamnan ta bari akan jihar a lokacin da wa’adinta ya ƙare.

Onanuga ya ce, a yanzu gwamnatin jihar ta gabatar da hujjoji masu nuna cewa ma’aikatan hukumar albarkatun ruwa ta jihar, malamai da ‘yan fansho da giratuti suna bin sa bashi kuɗaɗen albashi, kuma ya ciyo wasu basusuka da bai biya ba kafin ya sauka a mulki.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Anambara ta yanzu a ranar Talata, ta musanta iƙirarin nasa da cewa gwamnatin tasa ta bar basusuka ga gwamnatocin baya, ciki har da biliyan N2 na kuɗin tallafi, kuɗaɗen kwangiloli, albshin ma’aikatan da ba a biya su ba da kuma na ‘yan fansho da giratuti.

Obi dai a nasa ɓangaren ya ce gwamnatinsa ta biya kuɗaɗen giratuti da na bashin da ya tarar da jimillarsu ta kai biliyan N35 ba tare da barin bashin albashi, fansho ko giratuti ba.

Hakan na zuwa ne yayin da ɓangaren gwamnatin jihar na yanzu ya fitar da rahoton kuɗaɗen da ya sha bamban da wanda gwamnatin Obi ta fitar a lokacin da ya kammala shugabancin jihar a 2014.

By Babaji

Leave a Reply