Gwamnan Zamfara zai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal zai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, inda zai gana da shugabannin duniya, abokan hulɗa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin jawo zuba jari zuwa Jihar Zamfara.

Zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 na da taken, “Maido da Amincewa, Gudanar da Sauye-sauye: Majalisar Ɗinkin Duniya Mai Aiwatar da Ayyukanta Ga Kowa.”

Sanarwar ta fito ne daga Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a ranar 16 ga Satumba, 2026.

Manyan tarukan Majalisar Ɗinkin Duniya za su mayar da hankali kan Manufofin Ci Gaba Mai Ɗorewa (SDGs), yaƙi da sauyin yanayi, tunkarar annoba, adalcin launin fata da kuma kwance ɗamarar makaman nukiliya.

Halarcin gwamnan zai ba da damar gabatar da abubuwan da Zamfara ta sa a gaba na ci gaba, gina haɗin gwiwa da neman hanyoyin haɗin gwiwa kan tsaro, bunƙasar tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Ayyukan Gwamna Lawal za su fara ne ranar 18 ga Satumba, tare da wani babban taron shugabannin duniya na gefe da kuma taron SDG Moment.

A ranar 21 ga Satumba, Gwamna Lawal zai yi jawabi a wani babban taron gefe yayin zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ya shirya, mai taken, “Daga Rauni Zuwa Dama: Hanyoyin Da Al’ummomi Ke Jagoranta Wajen Samar da Zaman Lafiya, Juriya da Zuba Jari A Yankunan Da Ke Fuskantar Rauni.”

Taron zai ƙaddamar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci gaban Arewa maso Yamma na 2026 zuwa 2030, tare da taimakawa wajen gina dabarun haɗin gwiwa da zuba jari don tallafa wa aiwatar da shi.

Sauran muhimman tarukan sun haɗa da Tattaunawar Teburin SDG ta 2026, Taron Shekara-shekara na Clinton Global Initiative, da Babban Taron Tattaunawa tsakanin Afirka da Caribbean mai taken: “Sake Bayyana Tasiri, Gaggauta Aiki”, da kuma Taron Zuba Jari na Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply