NNPCL ya sake ƙara farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya sake ƙara farashin litar fetur a gidajen mansa da ke Abuja da kewayenta.

Ƙarin na kwanan nan ya yi sanadiyyar komawar farashin zuwa Naira 1,430 ga kowace lita, lamarin da ya ƙara shigar da matsin kuɗi kan masu ababen hawa da sauran kwastomomi da ke cigaba da jure wa hauhawar farashin fetur.

Gidajen mai da dama a Birnin Tarayya Abuja sun nuna cewa yanzu farashin litar ya koma tsakanin N1395 da N1,430. Sababbin farashin na wakiltar ƙarin N50 zuwa N80, bisa la’akari da gurin da gidan mai yake.

Tuni dai aka fara amfani da sababbin farashin a yankuna daban-daban, ciki har da Airport Junction, Gwarimpa, Kubwa Expressway da Wuse Zone 4 da kuma wasu sassan babban birnin da kewayensa.

Ana tsammanin wannan al’amari zai yi matuƙar tasiri ga farashin sufurin jama’a da kayayyaki musamman daga ɓangaren motocin ‘yan kasuwa.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan gidajen man MRS sun ƙara farashi zuwa N1,395 ga kowace lita bayan sauya farashi daga Matatar Ɗangote.

By Babaji

Leave a Reply