Yadda garin Kano ya samo sunansa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Daga cikin tsoffin biranen Hausa, Kano ta shahara a matsayin ɗaya daga cikin biranen da suka fi ɗauke da tarihi mai zurfi a Arewacin Nijeriya. Amma kafin a kira ta da sunan “Kano”, akwai wasu tsoffin matsugunai da al’ummomi a yankin, musamman a wajen Dutsen Dala. To, ina sunan Kano ya samo asali?

Tarihin garin Kano yana daga cikin tarihin da suka fi jan hankalin masu bincike a kan tarihin Hausawa. Birnin ya yi suna wajen kasuwanci, sana’o’i, ilimi, siyasa da kuma tsarin mulkin gargajiya, amma tambayar yadda aka samo sunansa har yanzu tana da ruwayoyi fiye da ɗaya.

A wasu daga cikin tsoffin bayanai, an ce yankin da daga baya ya zama Kano ya kasance da ƙananan matsugunai tun kafin zuwan Bagauda, wanda al’adar tarihi ta ɗauka a matsayin wanda ya kafa daular Kano ta farko a kusan shekara ta 999 Miladiyya. Daga cikin waɗannan tsoffin matsugunai akwai Dala, Magwan, Gwauron Dutse, Fanisau da Santolo.

Dala: Inda tarihin Kano ya fara samun tushe:

Daga cikin wuraren da suka fi muhimmanci wajen fahimtar farkon tarihin Kano akwai Dutsen Dala. Bayanai daga binciken tarihi sun nuna cewa Dala ta kasance muhimmiyar cibiyar zama da sana’o’i tun ƙarni na farko na tarihin yankin.

A cewar wasu ruwayoyi, mutanen da suka fara zama a yankin sun haɗa da mafarauta da masu aikin ƙarfe. Wasu daga cikinsu ana danganta su da Abagayawa, waɗanda aka ce sun yi ƙaura daga Gaya zuwa yankin Dala saboda neman ma’adinan ƙarfe. Wannan ya nuna cewa akwai rayuwar al’umma a yankin tun kafin samuwar daular Kano a ƙarƙashin sarakunan Bagauda.

A wannan zamani na farko, Dala ita ce aka fi danganta da yankin da daga baya ya zama birnin Kano. Wasu tsoffin bayanai ma sun nuna cewa ana kiran yankin da Dala har zuwa ƙarshen ƙarni na 15 da farkon ƙarni na 16, musamman a wasu bayanan da suka fito daga Borno.

Ruwayar Dala da Barbushe:

A cikin abin da aka fi sani da Kano Chronicle, wato Tarihin Sarakunan Kano, akwai ruwayoyi masu yawa game da farkon zaman mutane a yankin.

Kano Chronicle wani muhimmin rubutaccen kundin tarihi ne da ke ɗauke da jerin sarakunan Kano da labaran da suka shafi tarihin masarautar. Masana tarihi sun yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki dukkan bayanan cikinsa a matsayin tabbataccen tarihi kai tsaye ba, domin kundin ya haɗa rubutattun bayanai da al’adun baka da aka gada daga al’ummomin yankin.

A cikin wannan al’ada ta tarihi, an ambaci Barbushe, wanda ake danganta shi da Dutsen Dala. An bayyana shi a matsayin wani fitaccen mafarauci kuma jagoran al’ummar farko ta yankin, wadda ke da alaƙa da al’adun gargajiya kafin shigowar Musulunci da samuwar tsarin mulkin sarakunan Kano.

To, daga ina kalmar “Kano” ta fito?

A nan ne labarin ya fara zama mai ban sha’awa, domin akwai ruwayoyi daban-daban game da asalin sunan Kano.

ɗaya daga cikin ruwayoyin da aka fi sani ta danganta sunan Kano da wani mutum mai suna Kano, wanda ake cewa ya kasance daga cikin tsoffin mutanen da suka zauna a yankin Dutsen Dala.

Wata ruwayar kuma ta danganta sunan da Bagauda.

Bagauda shi ne wanda al’adar tarihin Kano ta ce ya zo yankin a kusan shekara ta 999 Miladiyya, daga bisani ya kafa tsarin mulkin da ya zama tushen Daular Kano. A wasu ruwayoyi, an ce Bagauda ya kasance yana da laƙabi ko suna na Yakano, kuma daga wannan laƙabi ne aka samo sunan “Kano”.

Wannan ita ce ɗaya daga cikin shahararrun bayanan da ake samu a cikin tarihin asalin sunan birnin.

Sai dai wasu bayanan tarihi sun kawo wata magana daban, inda suka danganta sunan Kano da wani tsohon maƙeri daga Gaya da ake kira Kano. An ce wannan mutum ya zauna a kusa da Dutsen Dala ne saboda neman dutsen ƙarfe, kuma daga sunansa aka samu sunan Kano.

Saboda haka, ba abu ne mai sauƙi ba a ce akwai mutum guda da aka tabbatar da hujjar tarihi cewa shi ne ya ba birnin sunan Kano.

Bagauda da sauyin tarihin yankin:

Zuwan Bagauda ya kawo wani sabon babi a tarihin yankin.

A cewar ruwayar Kano Chronicle, Bagauda ya zama Sarkin Kano na farko, kuma mulkinsa ya kasance daga kusan shekara ta 999 zuwa 1063. Daga baya zuriyarsa suka ci gaba da sarrafa masarautar.

Amma kafa Daular Kano ba yana nufin cewa kafin Bagauda babu wata al’umma ko tsarin rayuwa a yankin ba. A maimakon haka, akwai tsoffin matsugunai da al’ummomi waɗanda suka riga shi, sannan daga baya aka haɗa su cikin sabon tsarin siyasa da ya fara ƙarfafa Kano a matsayin masarauta.

Gijimasu da gina birnin Kano:

Wani muhimmin abin da ya ƙara sauya fasalin Kano shi ne zamanin Gijimasu, wanda aka bayyana a matsayin jikan Bagauda.

Bayanan tarihi sun nuna cewa Gijimasu, wanda aka danganta mulkinsa da shekarun 1095 zuwa 1134, shi ne ya fara gina katangar birnin Kano a ƙasan Dutsen Dala. Daga baya ɗansa, Tsaraki, ya kammala aikin katangar.

Wannan ci gaba ya nuna yadda wani yanki da ya fara a matsayin ƙananan matsugunai a kusa da Dala ya fara rikiɗewa zuwa birni mai cikakken tsari, mai katanga, ƙofofi, kasuwanni da cibiyoyin mulki.

Daga nan Kano ta fara samun ƙarin muhimmanci a matsayin cibiyar kasuwanci da siyasa, inda ’yan kasuwa, manoma, maƙera, mafarauta, malamai da masu sana’o’i daga sassa daban-daban suka riƙa shigowa.

Shin “Kano” sunan mutum ne ko sunan wuri?

Wannan tambayar ita ce har yanzu take sa batun asalin sunan Kano ya kasance mai ɗan ruɗani.

Wasu ruwayoyi suna cewa Kano sunan mutum ne daga cikin tsoffin mazauna yankin. Wasu kuma suna danganta shi da Yakano, laƙabin Bagauda. Wasu bayanai kuma suna nuna cewa Dala shi ne tsohon sunan yankin, kafin daga baya sunan Kano ya samu karɓuwa.

Masana tarihi kuwa sun nuna cewa tarihin Kano ya ƙunshi haɗuwar bayanan rubuce da al’adun baka, don haka wasu daga cikin labaran asalin sunan ba za a iya tabbatar da su kamar yadda ake tabbatar da bayanan da aka samu daga rubuce-rubucen zamani ba. Wani bincike na Jami’ar Cambridge ma ya yi nuni da irin wannan ƙalubalen wajen tantance tarihin da ke cikin Kano Chronicle.

Daga tsohon matsuguni zuwa babbar cibiyar Hausa:

Ko da yake ba a da cikakkiyar hujja guda da za ta kawo ƙarshen dukkan ruwayoyin da suka shafi asalin sunan Kano, abin da ba a musanta ba shi ne muhimmancin yankin Dala da tsoffin al’ummomin da suka rayu a cikinsa wajen samuwar birnin.

A hankali, Kano ta wuce matsayin ƙaramin matsuguni zuwa masarauta, sannan ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin siyasa, kasuwanci da ilimi a ƙasar Hausa.

Daga baya, ta zama muhimmiyar cibiyar kasuwancin nahiyar Afirka ta Yamma, musamman wajen fata, yadi, rini, hatsi da sauran kayayyaki. Hakan ya taimaka wajen sanya sunan Kano ya zama sananne a sassa daban-daban na Afirka.

Saboda haka, idan aka tambayi “Ta yaya Kano ta samo sunanta?”, amsar da ta fi dacewa ita ce: akwai ruwayoyi da dama, wasu suna danganta sunan da wani mutum mai suna Kano, wasu da laƙabin Bagauda na “Yakano”, yayin da tsohon yankin kansa ya taɓa kasancewa ana danganta shi da Dala.

Abin da tarihi ya tabbatar mana shi ne cewa Kano ba ta fara ne a matsayin birni ɗaya kwatsam ba. Ta samo asali ne daga tsoffin matsugunai da al’ummomi, musamman a kusa da Dutsen Dala, kafin zuwan Bagauda da samuwar masarautar Kano. Daga nan ne aka fara gina tubalin birnin da yau ya zama ɗaya daga cikin manyan biranen tarihi a Nijeriya.

Blueprint Manhaja za ta ci gaba da dawo da irin waɗannan labaran tarihi domin tunatar da masu karatu cewa bayan kowanne gari, suna da dutse, kasuwa ko unguwa da muke gani a yau, akwai dogon tarihi da ya cancanci a san shi, a adana shi kuma a ba shi muhimmancin da ya dace.

Madogaran bincikenmu:

1. Hunwick, John O. (1994). “A Historical Whodunit: The So-Called ‘Kano Chronicle’ and its Place in the Historiography of Kano.” History in Africa, Vol. 21, pp. 127–146. Wannan muhimmin bincike ne kan tarihin Kano Chronicle, musamman batun lokacin da aka rubuta ta da kuma yadda ya kamata masana su yi amfani da ita a matsayin madogarar tarihi.

2. Palmer, H. R. (1908). “The Kano Chronicle.” Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland, Vol. 38. Wannan shi ne sanannen tsohon bugu da fassarar Kano Chronicle zuwa Turanci, wanda ya taimaka wajen yaɗa bayanan tarihin sarakunan Kano ga masu binciken tarihi. 

3. Ki-Zerbo, Joseph & Niane, Djibril Tamsir (eds.). UNESCO General History of Africa, Volume IV: Africa from the Twelfth to the Siɗteenth Century. Wannan madogara ta UNESCO ta bayyana cewa kafin kafuwar birnin Kano akwai ƙananan masarautun al’ada a yankin Dala; sannan ta sanya shigowar Bagauda yankin Kano a kusan shekara ta 999, yayin da jikansa Gijimasu (1095–1134) ya kafa Kano a gindin Dala, ya fara gina katangar birni, wadda ɗansa Tsaraki ya kammala. 

4. Adamu, Abdalla Uba & Gwarzo, Bello Bashir (eds.) (2010). Kano in the Second Millennium: Selected Papers Presented at the Seminar on Kano in the Second Millennium. Research and Documentation Directorate, Government House, Kano. Littafin ya ƙunshi bincike daga taron masana da aka gudanar a Kano kan tarihin birnin, siyasa, tattalin arziki da zamantakewarsa.

By ukarofi

Leave a Reply