Shettima ya dawo Nijeriya bayan taron BRICS a Indiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Nijeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron jagororin ƙasashen BRICS da aka gudanar a birnin New Delhi na ƙasar Indiya.

A yayin ziyarar, Shettima ya shiga sahun tattaunawa da wakilan ƙasashe daban-daban kan muhimman batutuwan da suka shafi ci-gaba da nufin faɗaɗa damarmakin ci-gaban tattalin arziƙin Nijeriya da janyo ra’ayoyin ƙasashe a harkar difulomasiyya.

Kakakin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce, daga cikin hada-hadar da aka dama da Shettima akwai ganawarsa da Firaministan Indiya, Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabon tsarin kasuwancin ɗanyen mai, zuba jari, harkokin magani, tsaro, fasahar digital, fasahar zane, makamashi da wasu fannonin dabarun ci-gaba.

Haka kuma, ya bayyana cewa Shettima ya gana da Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, inda ya jaddada mata goyon bayan Nijeriya ga hulɗar haɗaka kan lamuran ci-gaban tattali da tsare-tsarensa a matakin duniya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma isar da saƙon Shugaba Tinubu na kira da a samar da gyare-gyare ga jagorancin duniya da cibiyoyin kuɗaɗe, yayin daidaita Nijeriya a matsayin cibiyar faɗaɗa kasuwancin Afirka a ƙarƙashin shirin “African Continental Free Trade Area”.

Har ila yau, Nijeriya ta yi amfani da damar taron wajen ƙarfafa hulɗa da ƙasashen BRICS da kuma ƙulla alaƙoƙi a fannonin noma, fasahar zamani ta AI, ababen more rayuwa na zamani, ƙere-ƙere, lafiya, makamashi da kuma ci-gaban lamuran inganta ɗan-adam.

By Babaji

Leave a Reply