
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumomin tsaro sun ɗauki matakan ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan makarantu, sansanonin horo na NYSC, wuraren ibada da wasu gurare masu sauƙin fuskantar hare-hare bayan samun wasu bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’adda suna shirin ƙaddamar da hare-hare a sassan Nijeriya.
A wani saƙon ankararwa da Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya ta fitar, wadda aka raba wa rassanta a faɗin ƙasar, hukumar ta yi gargaɗin shirin hare-haren da akwai yiwuwar a ƙaddamar da su a daidai lokacin da ake koma wa harkokin karatu na zangon 2026/2027.
A cewar sanarwar, bayanan sirri da aka fitar ga Sashen Atisayen rundunar sun nuna ‘yan ta’adda suna ƙoƙarin shirya wasu hare-hare a wuraren taron jama’a, ciki har da makarantu, wuraren ibada da makamantansu.
Tuni dai hukumar ta tura saƙon ankararwar tsaron ga jagororinta na shiyyoyi daga na 1 zuwa 17, rassa, masu ayyukan daƙile ta’addanci da wasu tawagogi da kuma kwamishinonin baki ɗaya jihohin Nijeriya da dai sauransu.
A cewar ‘yan sanda, bayanan sirri sun nuna cewa akwai zirga-zirgar ‘yan ta’adda daga Katsina zuwa Kaduna zuwa Jihar Filato. Haka kuma, ta ce mayaƙan ISWAP da masu taimaka musu suna aikin shirya ƙaddamar da wasu hare-hare a wasu muhimman wurare da suke hari.
Haka kuma, rundunar ta bayyana barazanar ga cibiyoyin ilimi a matsayin abin da aka fi damuwa a kai, tana mai gargaɗin yiwuwar hare-haren su dace da lokacin komawa karatu na zangon 2026/2027. Akan haka ne ta umarci dakarunta da su ƙarfafa tsaro a guraren da aka lissafa a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile aukuwar hare-haren.
Tuni dai Hedikwatar Tsaro ta ce tana sanya ido akan halin da ake ciki, kamar yadda Daraktan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja ya bayyana.
