Annobar Kwalara Da Mashaƙo: Mu ɗauki matakan kariya ga lafiyar iyalanmu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Ba sabon labari ba ne yadda cututtuka masu haɗari irin su cutar amai da gudawa (Kwalara) da Mashaƙo wacce a turance ake kira da difteriya, ke cigaba da barazana ga rayukan iyalai da dama a Nijeriya. Bincike ya nuna cewa a wannan shekara ta 2026 kaɗai, an riga an samu fiye da mutane 65,000 da ke fama da zazzaɓin cizon sauro, da kuma fiye da 10,000 da ke fama da difteriya. Wannan lamari ya sa dole a ƙara ɗaga murya da kira ga iyaye da masu kula da yara su ƙara himma da sa ido wajen kula da tsabta da ɗaukar matakan kariya don kare lafiyar ‘ya’yansu.

Kamar yadda mai yiwuwa muka sha ji daga bakin likitoci da ma’aikatan lafiya, cutar Kwalara, cuta ce mai saurin yaɗuwa a tsakanin jama’a, musamman waɗanda ke zaune a muhalli marar tsafta ko kuma cikin cinkoso, kamar misalin unguwannin talakawa da ake cakuɗe da juna. Cuta ce harwayau wacce ke shafar hanji, kuma tana farawa ne sakamakon sha ko cin abinci da ya lalace ko ruwa marar tsafta wanda ya gurɓata da ƙwayoyin cuta. Tana haifar da gudawa mai ruwa da kuma amai mai tsanani, wanda sanadiyyar fitar ruwa mai yawa daga jikin mutum zai iya kaiwa ga bushewar jiki (dehydration), har ma da mutuwa idan ba a yi magani ba da wuri ba.

Haka kuma ita cutar mashaƙo ta Difteriya, cuta ce mai saurin yaɗuwa wacce take shafar maƙogwaro da sarƙe numfashi idan ta yi tsanani. Ana ɗaukar cutar ne ta hanyar shaƙar numfashi juna, ko ta hanyar taɓa kayan da suka gurɓata da cutar. Alamominta sun haɗa da ciwon maƙogwaro, zazzaɓi, da wani farin abu mai kama da yaɗi a cikin maƙogwaro wanda ke sarƙe numfashi.

Bincike ya nunar da cewa, alamun cutar na iya fara bayyana ne bayan kwana 2 zuwa 5 da kamuwa da ita, amma wani lokaci tana iya ɗaukar har zuwa kwana 10, ba tare da an gane ita ba ce.

Daga cikin alamun farko akwai zazzaɓi, sau da yawa ba mai zafi sosai ba. Akwai ciwon maƙogwaro, akwai tari, mura ko fitar majina daga hanci. Sannan kuma yana sa idanu su yi ja ko su kumbura. Ana jin yawan kasala, raunin jiki ko rashin kuzari.

Akwai kuma ƙuraje a wuya ko kumburin gefen wuya, da wahalar haɗiye abinci ko ruwa. Sannan kuma za a lura da muryar yaro ta sauya ko ta yi kauri.

Alamar da suka fi saurin nuna cutar sun haɗa da samun wani kauri mai launin toka ko fari a saman makogwaro, kan ýar wuya, ko cikin hanci. Wannan kaurin bai kamata a sa wanzamai su cire shi da hannu ko wani abu ba, domin cire shi na iya jawo zubar jini kuma cutar na iya toshe hanyar numfashi. Haka kuma akwai kumburin wuya mai yawa, wanda zai iya sa wuyan yaro ya yi kauri sosai, shi ma alama ce mai tsanani. Cutar na iya cigaba da toshe maƙogwaro, ta sa yaro ya kasa haɗiye yawu ko yin numfashi, wani lokaci kuma za a ga yana yawan zubar da miyau.

Za kuma a ga leɓɓan yaro ko fuskarsa tana canza launi zuwa shuɗi. Jiki yaro ya yi rauni yana jin kasala sosai, idan ya yi tsanani ma har suma zai riƙa yi kuma ya kasa farkawa.

A duk lokacin da aka lura da waɗannan alamu da na yi bayaninsu a baya, abin da likitoci ke cewa shi ne a gaggata kai yaro asibiti ko wata cibiyar lafiya mafi kusa. Domin a wannan lokacin idan an lura za a ga numfashin yaro yana sarƙewa, yana wahalar fitar da iska ko jan numfashi. Sannan za a ji yana fitar da wani irin sauti mai kaifi yayin shaƙar iska, kamar mai gwarti. ƙirji yana faɗawa ciki yayin numfashi.

Ma’aikatan lafiya suna ba da shawara kan cewa, a duk lokacin da aka lura da waɗannan alamomi kada a jira alamun su yi tsanani. A ware yaron daga sauran yara, a tabbatar an raba masa wurin kwanciya, cokali, kofuna ko kayan ci, sannan a kai shi asibiti domin a yi masa gwaji, don a tabbatar kuma a ba shi magani. Kada a ba shi magani a gida ko a je kyamis, ba tare da shawarar ma’aikacin lafiya ba.

Daga cikin dalilan da ke kawo wannan cuta a cewar ma’aikatan lafiya shi ne idan ba a yi wa yaro rigakafi tun yana jinjiri ba, ko kuma an fara rigakafin sai aka kasa kammalawa, wannan yana sa cutar ta yi saurin kama shi. Don haka ko da an je asibiti a tabbatar an a sanar da ma’aikatan lafiya cewa yaron bai kammala allurar rigakafin sa ba. Rigakafi na daga cikin muhimman hanyoyin kariya, don haka iyaye su tabbatar da cewa yara sun karɓi allurar da jadawalin rigakafi ya tanada.

Abu ne mai muhimmanci a fahimci cewa, irin waɗannan cututtuka masu yaɗuwa ana kamuwa da su ne a dalilai na rashin tsafta, rashin kulawa da dokokin kiwon lafiya, da kuma rashin amfani da ruwan sha mai tsafta.

A wani rahoto da Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta ƙasa ta NCDC ta fitar an bayyana cewa, daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar sun haɗa da shan ruwa marar tsabta, rashin banɗaki mai tsafta a gida, rashin tsaftace tsakar gida akai akai, da kuma zubar da ƙazanta ko’ina a cikin gida. 

Akwai kuma rashin wanke hannu da sabulu kafin da bayan cin abinci, da rashin kula da tsafta a wuraren taruwar jama’a kamar kasuwanni da makarantu.

Gwamnatin Jihar Filato ta kasance ta farko a duk faɗin Nijeriya da ta sanar da rufe makarantu da dakatar da waɗanda ke shirin komawa bayan dogon hutu da yara suka yi, domin daƙile yaɗuwar cutar a tsakanin ɗalibai da malamai, da kuma ƙarfafa gwiwar mutane su riƙa sa takunkumin kare fuska a wuraren taruwar jama’a. 

Gwamnatin Tarayya a nata ɓangaren ta ɗauki matakan gaggawa don yaƙar waɗannan cututtuka, ciki har da tura allurar rigakafi fiye da 500,000 zuwa jihohin Kano, Katsina da Filato. Haka nan, ana aiwatar da shirye-shirye na tsaftace ruwa da kuma wayar da kan jama’a a faɗin kasa bakiɗaya. 

Sai dai duk da haka, nasarar waɗannan shirye-shirye ta dogara ne kan haɗin kan da iyaye da sauran al’umma suka bayar, kamar yadda mu ma muke yi ta wannan kafa. ’Yan Nijeriya su tabbatar sun kai yaransu da kawunan su wajen karɓar rigakafi da ake yi a unguwanni da asibitoci, don an ce rigakafi ya fi magani. A cewar Hukumar NCDC, “Difteriya cuta ce da za a iya kauce mata ta hanyar rigakafi.”

Kula da tsabta da ɗaukar matakan kariya ba wai kawai alhakin gwamnati ba ne, har ma alhakin iyaye ne da ma kowanne ɗan Nijeriya. Ta hanyar wanke hannu, shan ruwa mai tsabta, kula da tsaftar muhalli, da kuma tabbatar da cewa yara sun karɓi allurar rigakafi a lokacin suna jarirai, zai iya taimakawa wajenkare ‘ya’yanmu daga waɗannan cututtuka masu haɗari.

Kar a manta, “Tsabta ita ce rabin lafiya.” A koyarwar addini kuma mun sani cewa, “Tsafta ita ce cikon addini.” Don haka mu ɗauki wannan a matsayin shawara ta yadda za mu kare lafiyar ‘ya’yanmu da ƙasar mu bakiɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply