
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, ya ayyana makokin kwanaki uku a jihar bayan rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wato ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma ɗan asalin Jihar Adamawa.
Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026 bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci. Gwamnan ya yi wannan sanarwa ne a wata takarda da Sakataren yaɗa labaransa. Humwashi Wonosikou ya sanya wa hannu a Yola, babban birnin jihar.
Fintiri ya kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalan, abokan siyasa, abokan arziƙi, masu fatan alheri da ɗaukacin al’ummar Adamawa a madadin gwamnatin jihar bisa babban rashin. Ya bayyana rasuwar marigayin, wanda kuma shi ne tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a Jamhuriy ta Biyu kuma tsohon Ministan Ma’aikatar Masana’antu kuma Shugaban PDP na Ƙasa, a matsayin babban rashi ga Adamawa da ma Nijeriya baki ɗaya.
Haka kuma, gwamnan ya yaba wa ƙwarin-gwiwa, hangen nesa, kishi, hikima, ƙwarewa da tsawon ran Bamanga Tukur, wanda a cewarsa, ya yi amfani da su wajen hidimar ƙasa da al’umma za su yi kewa na tsawon lokaci.
Gwamna Fintiri ya tunatar da shawarwari da faɗakarwar da ya samu daga tsohon gwamnan kan harkokin shugabanci, waɗanda ya ce sun taimaka wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba da wasu ababe a jihar.
A ƙarshe, Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi koyi da ayyukan alherinsa wajen hidima da jagoranci, yana mai cewa rashinsa ya haifar da gagarumar giɓi da ka iya wahalar samun wanda zai maye shi.
