Daga USMAN KAROFI
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi alƙawarin kafa mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Sowore ya ce manufar jam’iyyar ta mayar da hankali ne kan tabbatar da adalci, daidaito da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya kuma yi alƙawarin samar da wutar lantarki na sa’o’i 24, da tabbatar da ilimi kyauta kuma mai sauƙin samu a dukkan matakai. Haka kuma, ya ce gwamnatin AAC za ta gina gidaje miliyan ɗaya masu sauƙin kuɗi tare da yin garambawul ga dokokin haya domin rage matsalar biyan kuɗin haya na shekaru ɗaya ko biyu a gaba.
Sowore ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan bunƙasa masana’antu da noma, samar da ayyukan yi, inganta ababen more rayuwa da yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce za a yi garambawul ga tsarin tsaro, a inganta jin daɗin jami’an tsaro tare da amfani da fasahohin zamani wajen yaƙi da laifuka. Ya kuma yi alƙawarin yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma dawo da kuɗaɗen gwamnati da aka wawure.
