NASEMA ta raba kayan agaji ga waɗanda hare-haren ta’addanci ya shafa a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukuma dake kula da aukuwar gaggawa wato Nasarawa State Emergency Management Agency (NASEMA) a turance ta raba kayayyakin agaji na miliyoyin kuɗi ga waɗanda bala’oin rayuwa daban daban suka shafa da suka haɗa da hare-haren ta’addanci da rigingimun ƙabilanci da rigingimun filaye da ambaliyar ruwa da gobara da sauran su a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomi uku wato Akwanga da Wamba da kuma Nasarawa Eggon duka a jihar ta Nasarawa.

Wakilin mu da ya kasance a wajen rabon ya rawaito cewa kayayyakin agajin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa da na wake da katon-katon na taliya da man-gyaɗa na abinci da katifu da magi da gishiri da sauran su.

Da yake jawabi a yayin rabon, darakta janar na hukumar NASEMA ɗin a jihar ya bayyana cewa don rage ƙunshi da waɗanda tashin-tashinan ya shafa suka sami kansu ne yasa hukumar ta ƙasa wato NEMA ta reshen ta na shiyar Arewa ta tsakiya ta ga ya dace ta gabatar da agajin ga Nasema don a raba wa waɗanda lamarin ya shafa a yankin.

Yace” Idan zaku iya tunawa kimanin watanni uku da suka gabata an samu wasu munanan bala’oi da suka haɗa da ambaliyar ruwa da sace-sacen mutane da harin ‘yan ta’adda da rigingimun ƙabilanci da na filaye da sauran su a waɗannan ƙauyuka uku da ke yankin ƙaramar hukumar Akwanga da Wamba da Nasarawa Eggon Inda aka yi asarar dukiyoyi da sauran su.

“Akan haka nema ya sa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ga ya dace a taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa don rage musu wahalhalu da suka tsinci kansu inda ya turo waɗannan kayayyakin ta hukumar NEMA na ƙasa zuwa tamu ta jihar nan wato NASEMA, inda mu kuma muke gabatar muku a yanzu.

“A yanzu haka sauran ƙananan hukumomin biyu wato Wamba da Nasarawa Eggon suma an riga an aiko musu nasu.

“Ina kuma so inyi amfani da damar nan in yaba wa gwamnan talakawa Injiniya Abdullahi Sule dangane da gagaruman gudumawa da ya daɗe yana bayar don tallafi wa mabuƙata jihar baki ɗaya kana ina kuma bukaci wadanda suka amfana su tabbatar sunyi amfani da kayayyakin.” Inji shi.

A nasa ɓangaren wakilin NEMA a shiyar Arewa ta tsakiya da ke da ofishi a Jos jihar Filato Mista Audu Yohanna bayan ya gabatar wa NASEMA kayayyakin ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu jim kaɗan bayan ta samu lamarin mummunan lamarin ne sai tayi Allah-wadai tare da aiko kayayyakin agajin nan take don a raba su ga mabuƙatan inda ya roƙi waɗanda ba su samu a karon nan ba du yi haƙuri kasancewar za a cigaba da samar da tallafin.

Tun farko da yake jawabin Maraba, Shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, Safiyanu Isah Andaha wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Basau Ibrahim Shauibu ya jinjina wa hukumar NEMA tare da NASEMA dangane da tallafin, inda yace ƙaramar hukumar za ta cigaba da ba su cikakken gudumawa don tabbatar suna cigaba da cimma burin su.

Da yake sa albarka a rabon, Mai Martaba Chun-Mada wato sarkin Mata, Samson Gamuyare ya yaba wa hangan nesa da NEMA da NASEMA suka yi na kawo ɗauki wa waɗannan da yace basu ji ba ba su gani ba bala’in ya rutsa dasu.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da aka tattauna da su duk sun gode wa hukumomin dangane da tunawa da su a lokacin nan na alhinin su kana suka yi alƙawarin yin amfani da kayayyakin yadda ya dace.

By ukarofi

Leave a Reply