Zamfara: Rundunar sojoji ta musanta sace malamai a gidan Yari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojojin Nijeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani ayarin malamai a gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke jihar.

Saidai, ta tabbatar da rahoton awon-gaba da wasu mutane da ke tafiya daga yankin dajin Sububu a Ƙaramar Hukumar Bakura zuwa Talata Mafara.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na riƙo na Sashi na 2 na dakarun Atisayen FANSAR YAMMA, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar a ranar Lahadi, rundunar ta bayyana rahotannin da ake danganta garkuwa da gidan Yari da su a matsayin ƙarya abin ruɗarwa da ba shi da asali.

Osoba ya ce, rundunar sojin tana sane da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da dama, inda ta ce akwai buƙatar ta warware abin da ba haka ainihinsa yake ba. Ya bayyana cewa, “babu wani malami da aka sace a gidan Sanata Yari,” sannan gurin da aka ce a nan aka yi garkuwar, ba daidai ba ne. A cewarsa, bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa, an sace wasu mutane ne da ke kan hanyar tafiya daga yankin dajin Sububu a Bakura zuwa Talata Mafara.

Sannan, jami’an tsaro sun fara gudanar da aikin binciken gano inda aka garzaya da su da kuma ceto su, yana mai ƙarawa da cewa, sojoji da haɗin-gwiwar wasu hukumomin tsaro da ‘yan sa kai suna gudanar da atisaye a yankin. Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a sassan Jihar Zamfara, inda miyagun ayyuka suka yawaita a yankunan dazuka da wurare masu sauƙin fuskantar hare-haren garkuwa da wasunsu.

Akan haka ne rundunar ta kirayi jama’a da su ƙaurace wa aiki ko yaɗa rahotannin da ba su da tabbas ko waɗanda ba a tantance su ba, waɗanda a lokuta da dama su kan haddasa firgici acikin al’umma ko zama ƙalubale ga harkokin atisayen sojoji.

Haka kuma, ya yi kira ga mazauna da jagororin al’umma da su cigaba da kasancewa masu lura da sanya ido kan ababen da ke kai-kawo a yankunansu tare da sanar da hukumomin tsaro bayanai masu amfani akan lokaci da za su taimaka wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Kazalika, rundunar ta ce hedikwatar Shiyya ta 8 da Sashi na 2 da FANSAR YAMMA suna cigaba da ƙoƙarin bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyin fararen hula a sassan Arewa maso Gabas, tana mai kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro haɗin kai domin shawo kan al’amarin a shiyyar.

By Babaji

Leave a Reply