Wani mutum ya kashe ƙaninsa sakamakon wani rikici da ya ɓarke a tsakaninsu kan irin albasa a garin Barkeji, da ke ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne ranar Talatar makon da ya gabata, inda Hadi Barkeji ya kashe ƙaninsa, Malam Shehu Barkeji, bayan wata taƙaddama da ta shafi irin albasa.
Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne bayan Shehu ya ɗauki irin albasa da ɗan uwansa Hadi ya ajiye domin amfani da shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, an kama wanda ake zargi da aikata kisan, kuma an miƙa shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin gudanar da cikakken bincike.
Ya ce, rundunar za ta tabbatar da an gudanar da bincike tare da bin matakan da suka dace domin tabbatar da adalci.
Tuni aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Shugabannin al’ummar Barkeji sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa ɗaukar doka a hannunsu.
