Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa talakawan Nijeriya, ciki har da direbobi, masu girki da ma’aikatan gida, za su samu damar mallakar hannun jari a Matatar Mai ta Dangote mai darajar dala biliyan 20.
Dangote ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas, yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron rattaba hannu kan yarjejeniyar fara sayar da hannun jarin matatar mai tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana.
Ya ce, manufar shigar da matatar cikin kasuwar hannayen jari ita ce tabbatar da cewa mallakarta ba ta tsaya ga attajirai da manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗi kaɗai ba.
“Abin da muke ƙoƙarin cimma shi ne tabbatar da cewa direbobinmu, masu girkinmu, ma’aikatan gidanmu da kowa ya samu damar mallakar hannun jari a matatar,” inji Dangote.
Taron ya samu halartar wasu manyan ’yan kasuwar kuɗi da masana harkokin zuba jari, ciki har da Shugaban Bankin Zenith, Jim Ovia, da Shugaban Heirs Holdings, Tony Elumelu.
A yayin sayar da hannun jarin, matatar za ta bayar da hannun jari na yau da kullum guda biliyan 4.1, kowannensu da darajar dala 0.000013, a farashin naira 525 ga kowane hannun jari.
Wannan ne karon farko da Matatar Mai ta Dangote za ta shiga kasuwar hannayen jari tun bayan ƙaddamar da ita a shekarar 2023, bayan shafe kusan shekaru 10 ana aikin gina ta tare da zuba jari da ya kai kusan dala biliyan 20.
Matatar, wadda ke yankin Lekki Free Zone a Jihar Legas, tana da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana, abin da ya sa ta zama matatar mai mafi girma da ke da layin tace mai guda ɗaya a Afirka.
Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya ta amince da fara sayar da hannun jarin, matakin da kamfanin ya ce ya buɗe ƙofa ga abin da ka iya zama ɗaya daga cikin manyan mu’amalolin kasuwar jari a tarihin Nijeriya. Wani jami’in kamfanin ya ce ana sa ran za a fara sanya hannun jarin matatar a kasuwar hannayen jari ranar 14 ga Satumba.
Kamfanin ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen da za a samu daga sayar da hannun jarin wajen faɗaɗa matatar, domin ƙara ƙarfin sarrafa ɗanyen mai daga matakin da take aiki da shi a yanzu na ganga 700,000 a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana.
Idan aka cimma wannan buri, matatar za ta zama mafi girma a duniya cikin matatun da ke aiki, inda za ta zarce katafaren rukunin matatun Jamnagar na Indiya. Wannan sabon yunƙurin tara jari ya biyo bayan zuba jarin masu zaman kansu na dala biliyan 2.5 da aka kammala a watan Yulin 2026.
A farashin naira 525 kan kowane hannun jari, ana hasashen ƙimar kasuwar Matatar Mai ta Dangote za ta kai kusan dala biliyan 47. Idan aka sayar da dukkan hannun jarin da aka tanada, shigar matatar cikin kasuwar hannayen jarin Nijeriya ka iya ƙara jimillar ƙimar kasuwar hannayen jarin NGɗ da kimanin kashi 30 zuwa 40.
An ƙaddamar da Matatar Mai ta Dangote a hukumance a watan Mayun 2023. A halin yanzu, matatar na samar da sama da kashi 80 cikin 100 na buƙatar man fetur da Nijeriya ke da shi a cikin gida. Sai dai ribar da ake sa ran samu a dogon lokaci za ta dogara ne kan samuwar ɗanyen mai da ake buƙata domin sarrafa shi, ƙaruwar fitar da man da aka tace zuwa ƙasashen waje da kuma farashin tace man a kasuwa.
Bayanan Hukumar Kula da Kuɗaɗen Raya Afirka sun nuna cewa ƙasashen Afirka na kashe sama da dala biliyan 230 a kowace shekara wajen shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, yayin da man fetur da aka tace ke wakiltar sama da kashi 70 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a yankin.
ƙungiyar Dangote na ƙoƙarin amfani da ƙarfin matatar wajen rage wannan gibi na samar da man fetur a Afirka tare da rage dogaro da shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje.
A wani ɓangare na faɗaɗa harkokinta, ƙungiyar ta kuma shirya fara aikin gina wata sabuwar matatar mai da za ta iya tace ganga 700,000 a kowace rana a yankin gabar teku na Lamu a Kenya, inda ake sa ran aza harsashin ginin ranar 30 ga Satumba.
Ana kallon fara sayar da hannun jarin Matatar Mai ta Dangote ga jama’a a ranar 14 ga Satumba a matsayin wani muhimmin gwaji ga yawan kuɗaɗen da ke yawo a kasuwar hannayen jarin cikin gida, da kuma yadda masu zuba jari za su nuna sha’awarsu ga manyan kadarorin masana’antu.
