Firaministan Iraƙi, Ali al-Zaidi, na fuskantar babban ƙalubale wajen ƙoƙarin kwance damarar wasu ƙungiyoyin Shi’a masu ƙarfin gaske da ke da alaƙa da Iran, duk da alkawarin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa gwamnatinsa za ta mayar da makaman ƙasar ƙarƙashin ikon gwamnati.
Zaidi ya yi wannan alƙawarin ne bayan ganawarsa da Trump a Fadar White House a watan Yuli, inda ya ce za a kammala aikin kwance damarar waɗannan ƙungiyoyi zuwa ranar 30 ga Satumba. Wannan rana ita ce kuma lokacin da aka shirya sojojin ƙawancen ƙasashen duniya da Amurka ke jagoranta za su kammala ficewarsu daga Iraƙi, lamarin da ya sa batun makaman ƙungiyoyin ya ƙara zama mai muhimmanci ga makomar tsaron ƙasar.
Sai dai ƙungiyoyin da ake magana a kansu ba su nuna alamar amincewa da shirin ba. Wasu daga cikinsu sun dade suna alaƙa da Iran, kuma sun kasance suna kai hare-hare kan muradun Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. Yanzu haka, yayin da ake ci gaba da yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran, shugabannin waɗannan ƙungiyoyi na ganin cewa lokaci bai yi da za su ajiye makamansu ba.
Wannan ne ya sa Zaidi ya shiga wani yanayi mai matuƙar sarkakiya. A gefe guda, yana samun goyon bayan Amurka fiye da yadda shugabannin Iraƙi da dama suka samu a baya, amma a gefe guda kuma dole ne ya yi la’akari da irin tasirin da Iran ke da shi a Iraƙi. Iran ta gina ƙarfi sosai a cikin ƙasar ta hanyar alaƙarta da ƙungiyoyin Shi’a masu ɗauke da makamai da kuma wasu ‘yan siyasar ƙasar, abin da ke nufin cewa duk wani mataki mai tsauri daga gwamnatin Zaidi na iya jefa ta cikin rikici da waɗanda ke da tasiri a cikin tsarin siyasar ƙasar.
An riga an ga yadda wannan matsalar za ta iya zama. A ranar 17 ga Agusta, jami’an rundunar musamman da ke ƙarƙashin umarnin firaministan kai tsaye sun kama shugaban leƙen asirin Harakat al-Nujaba, wata ƙungiya mai alaƙa da Iran wadda Amurka ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci. An zarge shi da hannu wajen kai hare-haren jirage marasa matuƙa kan muradun Amurka, kamar yadda wata takardar tsaro da Reuters ta gani da kuma wasu jami’an gwamnati uku suka tabbatar.
An tsare mutumin na tsawon sa’o’i 48, amma lamarin ya haifar da barazanar ramuwar gayya daga ƙungiyar, lamarin da ya tilasta wasu manyan ‘yan siyasar Shi’a shiga tsakani domin rage zafin rikicin. Bayan mako guda kuma, jami’an rundunar musamman ta Iraƙi sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi mambobin ƙungiyoyin mayaka ne, ciki har da wani kwamandan yankinsu, bisa zargin taimaka wa wajen shirya hare-hare kan muradun Amurka.
