Attajirin ɗan Nijeriya ya mutu bayan tiyatar ƙara girman mazaƙuta a Thailand

Spread the love

Komai na mutum yana da iyaka, kuma neman abin da ya wuce ƙaddarar halitta kan iya kai mutum inda bai yi zato ba, kamar wata karin magana da ke cewa, “garin neman ƙiba, akan nemo rama”. Wannan ce ke bayyana akan abin da ya faru da Mista Igho Tiny Ubiribo, wani attajirin ɗan kasuwar Birtaniya kuma ɗan asalin Nijeriya, wanda wata tafiyar jin daɗi da ya kai Thailand tare da matarsa ta sauya salo zuwa labarin mutuwa mai ɗaukar hankali.

Attajirin ɗan kasuwar kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, wanda aka fi sani da Denisi ko Ego, ya rasu yana da shekara 43 bayan ya yi wani aikin ƙara girman al’aura a lokacin wata tafiya ta jin daɗi da ya kai ƙasar Thailand tare da matarsa, Danielle Simba Allen.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayanan da aka gabatar a gaban Kotun Binciken Mutuwar Mutane ta Inner West London sun nuna cewa an yi wa Igho allurar sinadarin hyaluronic acid mai yawan mililita 40 tare da lidocaine a wani asibitin sirri da ba a bayyana sunansa ba a Thailand a watan Maris.

Daga baya an gano cewa wannan aikin ne ya janyo masa matsalar toshewar jijiyar huhu (pulmonary embolism), wadda daga ƙarshe ta yi sanadin mutuwarsa.

Bayan kammala aikin, an ce Igho da matarsa sun je yin tausa a otal ɗinsu na Marriott da ke Bangkok, inda ya fara ƙorafin ciwon ƙirji sannan ya faɗi har sau biyu kafin a garzaya da shi zuwa Asibitin Sukhumɓit.

Rahotanni sun ce da farko yana cikin hayyacinsa, amma daga baya yanayinsa ya tsananta inda ya suma kafin a samu damar gudanar da gwajin CT Scan da likitoci suka tsara masa.

Bayan bincike, likitoci sun gano cewa yana fama da toshewar jijiyar huhu, inda aka kai shi sashen kulawa ta musamman (ICU). Ma’aikatan lafiya sun yi ƙoƙarin farfaɗo da shi na tsawon fiye da mintuna 100, amma abin ya ci tura, inda ya rasu da sanyin safiyar ranar 6 ga Maris.

Binciken gawarsa da aka gudanar a Birtaniya daga baya ya gano wasu ƙwayoyin halitta a cikin huhunsa da suka yi daidai da sinadarin hyaluronic acid da aka yi amfani da shi wajen aikin.

Mai binciken musabbabin mutuwar, Jean Harkin, ta yanke hukuncin cewa aikin gyaran jiki da aka yi wa Igho ne ya haddasa toshewar jijiyar huhu wanda ya kai ga mutuwarsa.

Bayan yaɗuwar labarin a kafafen sada zumunta, wasu masu amfani da intanet sun bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.

Wani mai suna thecuteabiola ya ce: “Kuɗin da ban samu ba ne yake cetona daga shiga irin wannan hali.”

Haka kuma, officiallizdasilɓa ta rubuta cewa: “Ya kamata a kama wanda ya sa yake tunanin dole ne ya ƙara girman al’aurarsa.”

Wani mai suna only1daddyess ya ce da yana da isasshen kuɗi da tuni shi ma ya yi irin wannan aikin, amma yanzu zai ci gaba da rayuwa da abin da yake da shi.

Wasu kuma sun bayyana cewa neman canja halittar jiki saboda biyan bukatun wasu na iya jefa mutum cikin haɗari.

By ukarofi

Leave a Reply