“Wace ce matar da ta taimaka wajen kafa IET, ta haɗa mata a ƙarƙashin FOMWAN”
Daga AISHA ASAS
Ci gaba daga makon jiya.
Me ya sa ta kafa FOMWAN?
Bari mu koma wani muhimmin sashe. Shin Aisha Lemu ta gamsu da aikinta a makarantu da IET, ko ta ga akwai wani babban giɓi da ya shafi matan Musulmin Najeriya?
A shekarar 1985, Aisha Lemu tare da wasu mata musulmai suka kafa Federation of Muslim Women’s Associations in Nigeria, wato FOMWAN. An zaɓe ta a matsayin Amirah ta farko ta ƙasa, kuma ta yi wannan wa’adi na tsawon shekaru huɗu. Manufar ƙungiyar ita ce ta samar da wata babbar murya da za ta haɗa ƙungiyoyin mata musulmai daga sassa daban-daban na Najeriya, tare da ƙarfafa ilimin mata da ’yan mata da sauran ayyukan ci gaban al’umma.
Wannan mataki ya ƙara nuna irin yadda Aisha ke kallon ilimi. A wurinta, ba wai a koyar da mace kawai yadda za ta karanta littafi ba ne; ya kamata ilimi ya ba ta damar fahimtar addininta, tarbiyyantar da ’ya’yanta, shiga cikin ci gaban al’umma da kuma sanin hakkokinta da nauyin da ke kanta. Saboda haka FOMWAN ta zama wata hanyar da ta taimaka wajen faɗaɗa aikin da Aisha ta fara a makarantu zuwa matakin mata a faɗin ƙasa.
Bayan shekaru huɗu da ta yi a matsayin Amirah ta farko, ko Aisha ta dasa aya a ayyukan da suka jiɓinci mata gaba ɗaya?
Ko kaɗan Hajiya Aisha ba ta ja baya daga namijin ƙoƙarin da take yi wa mata ba. Domin ko bayan ta bar shugabancin FOMWAN, ta ci gaba da aiki a kan batutuwan mata, yara, ilimi da Da’wah, tare da rubuce-rubuce da halartar tarurruka. Wannan ya nuna cewa abin da ta yi wa mata bai ta’allaƙa da kujera ko muƙami ba. Ta ci gaba da bayar da gudunmawa ta hanyar ilimi da rubutu, yayin da FOMWAN da aka kafa ƙarƙashin jagorancinta ta ci gaba da faɗaɗa aikinta a matsayin ƙungiyar mata musulmai ta ƙasa.
Bari mu koma ɓangaren yara. Shin wace irin gudunmawa Aisha Lemu ta bayar kan rayuwa da tarbiyyar yara a matsayin wani ɓangare na gyaran al’umma?
Yara sun kasance cikin muhimman batutuwan da ta yi aiki a kansu. Ta rubuta kuma ta gabatar da ayyuka kan tarbiyyar yara, koyar da ɗabi’a da yadda ya kamata a koyar da Musulunci ga yara. Ta kuma kafa Almajiri Literacy Initiative, wato ALI, shirin da ya taimaka wa ɗaruruwan yaran almajirai a Jihar Neja wajen samun ilimin karatu da rubutu. Wannan ya nuna cewa tunaninta game da ilimi bai tsaya ga waɗanda suka riga suka samu damar shiga makaranta ba; ta kuma nemi hanyoyin isa ga yaran da tsarin ilimi na yau da kullum bai kai gare su ba.
A nan ne falsafar aikinta ta ƙara bayyana. Aisha ta yi amince cewa ilimi ne ya kamata ya canza rayuwa. Saboda haka, a wurinta karatu da rubutu ba su kasance wani abu na takarda kawai ba; hanya ce ta buɗe wa yaro ƙofa zuwa wata makoma daban. Wannan shi ya sa aikin da ta yi ga yara da almajirai ya cancanci a ɗauke shi a matsayin muhimmin sashe na gadon da ta bari, ba ƙaramin aiki a gefen sauran ayyukanta ba.
Aisha malamar Musulunci ce mai zurfin aiki a fannin da’wah. Ko hakan ya hana ta shiga batun fahimtar juna tsakanin mabiya addinai?
Zancen zaman lafiya tsakanin addinai ya zama wani sashe da ta taka rawar gani. Ta yi rubuce-rubuce da gabatar da takardu kan inter-faith relations, wato hulɗa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai. Daga cikin ayyukanta akwai Revelation and the Scriptures: An Islamic Perspective, yayin da wasu daga cikin ayyukan IET suka shafi ƙoƙarin gina fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci.
Wannan ɓangare na da muhimmanci duba da yadda yake nuna Aisha a matsayin mace mai ganin ilimi a matsayin gada tsakanin mutane. Ba ta ɗauki sanin Musulunci a matsayin dalilin ƙin fahimtar wanda ba musulmi ba; a maimakon haka, ta yi amfani da ilimi wajen ƙara fahimtar juna. Wannan ya dace da yadda rayuwarta ta fara tun tana Ingila, lokacin da ta fara tambaya da bincike kan addinai daban-daban kafin ta samu amsar da ta gamsar da ita a Musulunci.
Ko akwai wasu ƙalubale da ta ci karo da su saboda kawai tana mace?
Wannan wata tambaya ce da ba za a iya barin ta a cikin tarihin Aisha Lemu ba. A wane yanayi ne kasancewarta mace ta sa tafiyarta ta fi buƙatar haƙuri da jajircewa?
Ta yi rayuwa a lokacin da mata ba su da damar da suke da ita a yau a fannonin ilimi, jagoranci da harkokin addini. Duk da haka, ta zama shugabar makarantu, ta shiga aikin gyaran manhajar Islamic Studies, ta kafa babbar ƙungiyar mata musulmi ta ƙasa, ta zama Amirah ta farko, ta rubuta littattafai da dama, sannan ta jagoranci ayyukan ilimi da Da’wah. Wannan ba tafiya ce da za a iya yi ba tare da ƙalubale ba, musamman ga mace da ta shiga fannonin da galibi maza suka fi mamaye su.
Amma Aisha ba ta yi ƙoƙarin amfani da abin da take da shi, wato ilimi, rubutu, koyarwa, tawali’u da jajircewa, wurin fahimtar da al’umma musamman masu ganin ba ta cancanci ta yi abinda take yi ba inda ta dosa, kuma ba ta zo da niyyar kawo sabon abu ba. Ta gina tasirinta da fahimta a hankali. Wannan shi ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa labarinta ya zama abin koyi ga mata, ba wai kawai ta shiga wani wuri ba, ta yi amfani da damar da ta samu wajen buɗe hanya ga waɗanda za su zo bayanta.
Idan za mu tsaya mu duba rayuwarta gaba ɗaya, me za mu iya cewa ta cimma?
Ta yi aiki a matsayin malamar makaranta da shugabar makarantu a Kano, Sokoto da Minna. Ta taimaka wajen gyaran manhajar Islamic Studies, ta rubuta littattafai da kayan koyarwa da suka kai ga ɗalibai da malamai, ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa IET, sannan ta kafa FOMWAN tare da wasu mata musulmai kuma ta zama Amirah ta farko. Ta kafa Almajiri Literacy Initiative, ta yi aiki kan batutuwan yara, mata da hulɗar addinai, sannan ta kafa Association of Model Islamic Schools in Nigeria (AMIS), inda ta zama shugabar ƙasa ta farko daga 1998 zuwa 2000.
A ɓangaren girmamawa kuma, ta samu kyaututtuka da dama, amma ɗaya daga cikin manyan karramawar da ta samu ita ce Member of the Order of the Niger (MON), wadda aka ba ta a shekarar 2000 daga gwamnatin Najeriya. Duk da haka, idan aka auna rayuwarta da lambar yabo kawai, za a rasa babban abin da ta bari. Girmanta ya fi bayyana ne a cikin cibiyoyin da ta taimaka wajen kafawa, littattafan da ta rubuta, mata da ta ƙarfafa, yara da ta taimaka musu, da kuma ɗaliban da suka koya daga ayyukanta.
Bayan shekaru masu yawa a IET, yaushe Aisha Lemu ta kai ƙarshen babban aikinta a cibiyar da ta taimaka wajen kafawa?
Ta kasance Director General ta Islamic Education Trust har zuwa shekarar 2018, lokacin da Alhaji Arzika Rimau ya karɓi wannan matsayi. Wannan ya nuna tsawon lokacin da ta yi tana cikin ginin IET tun daga farkon kafuwarta a shekarar 1969. Fiye da shekaru arba’in bayan kafa cibiyar, har zuwa lokacin Aisha tana cikin jagorancin aikinta, tana kallon yadda abin da aka fara a matsayin wata ƙungiyar ilimi ya faɗaɗa zuwa makarantu, wallafe-wallafe, da’wah da ayyukan jin daɗin al’umma.
Yaushe Aisha Lemu ta yi wafatti?
Larabawa suna wani karin magana da cewa “lii kulli nihayatin bidda’a” Bahaushe kuwa ya ce komai ya yi farko zai yi ƙarshe. A ranar 5 ga Janairun 2019, Aisha Lemu ta rasu a Minna, Jihar Neja, tana da shekaru 78 ko 79 bisa yadda aka lissafa shekarunta a wasu bayanai. Ta bar mijinta, Sheikh Ahmed Lemu, ’ya’yanta Nuruddeen da Maryam Lemu da jikokinta. Rasuwarta ta jawo alhini a tsakanin al’ummar musulmi, ƙungiyoyin mata da mutanen da suka san gudunmawarta ga ilimi da da’wah. FOMWAN ta bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga harkar mata musulmi, yayin da wasu daga cikin waɗanda suka san ta suka yi magana kan iliminta, tawali’unsa da jajircewarta.
Idan mutum ya rasu, mene ne ya rage daga rayuwarsa?
Kamar yadda wani hadisi ya tabbatar, “idan bawa ya mutu, dukan ayyukansa suna tsayawa in banda uku. Yaro na gari da yake masa addu’a, ilimin da ya koyar, ko sadaka mai gudana.” A ɓangaren Aisha Lemu amsar tana cikin kowane ɓangare daga ɓangarorin uku. IET da aka kafa a shekarar 1969 har yanzu tana aiki a fannonin da’wah, ilimi da jin daɗin al’umma. FOMWAN da ta kafa a shekarar 1985 ta ci gaba da haɗa mata musulmi a Najeriya. Littattafanta suna ci gaba da kasancewa cikin kundin ayyukan Islamic Education Trust, yayin da wasu daga cikinsu suka zama kayan karatu da koyarwa. Ayyukanta kan mata, yara, da’wah da hulɗar addinai kuma sun bar wani tunani da ya wuce lokacin da take raye. Ga uwa uba ‘ya’ya da ta bari waɗanda ake kyautata wa zato da kuma ƙoƙarin taka sawun mahaifiyarsu.
