Tinubu ya buƙaci a yi wa jagorancin duniya da tsare-tsaren kuɗi kwaskwarima a taron BRICS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a samar da gyara na gaggawa na gyare-gyare ga tsare-tsaren jagorancin duniya da na harkokin kuɗi na ƙasa-da-ƙasa, yana mai cewa wajibi ne sharuɗɗan da ke tafiyar da harkokin su dace da halin tattalin arziƙi da bambance-bambancen wurare.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Lahadi ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, a taron jagororin ƙasashen BRICS da ke gudana a New Delhi na ƙasar Indiya.

A wata sanarwa da Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya fitar, Tinubu ya ce Nijeriya tana bayar da gudummawa ga tsarin duniya mai kiyaye wakilci da daidaito, ciki har da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da cibiyoyin kuɗi na ƙasa-da-ƙasa.

Ya ce, taron BRICS na ɗaga muryar ƙasashe masu tasowa da kuma tsarin damawa da ɓangarorin doka na ƙasa-da-ƙasa tare da kiran da Nijeriya ke yi ga cibiyoyi masu ƙoƙarin dacewa da halin tattalin arziƙi da ƙasa.

Haka kuma, Shugaban ya yi kira ga samun haɗin kan BRICS ga faɗaɗa harkokinta sa da tattaunawa ta yadda za a aiwatar da manufofinta a aikace domin bunƙasa ci-gaba acikin mambobin ƙasashe.

Har ila yau, shugaban ya yi amfani da damar taron wajen janyo ra’ayoyin masu zuba jari da su yi amfani da damarmakin da Nijeriya take da su na dabarun ci-gaban harkokin kasuwanci a nahiyar Afirka.

By Babaji

Leave a Reply