Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Masu ruwa da tsaki a Jihar Katsina sun samu damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma gabatar da shawarwari kan yadda ya kamata a tsara kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027.
An gudanar da zaman a ɗakin taro na yan jarida da ke majalisar dokokin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, inda wakilan ƙungiyoyin fararen hula da sauran mahalarta suka nemi ƙarin haske kan abubuwan da aka tanada a cikin kasafin, tare da jaddada buƙatar fifita ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma.
Shugaban kwamitin kasafi na Majalisar, Hon. Lawal H. Yaro, ya bayyana cewa sauraron ra’ayoyin jama’a wani muhimmin mataki ne kafin kammala aikin kasafin.
Ya ce majalisar za ta yi la’akari da shawarwarin da aka gabatar yayin da take ci gaba da nazarin ƙudirin.
A cewar Hon Yaro, majalisar za ta fara sauraron bayanan ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan kasafinsu nan gaba.
Taron ya samu halartar mataimakin kakakin majalisar, Hon. Abduljalal Haruna Runka, da sauran ’yan majalisa, jami’an gwamnati da wakilan ƙungiyoyin fararen hula.
