Dakarun tsaro sun halaka gomman ‘yan ta’adda bayan afka wa maɓoyarsu a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Haɗakar jami’an tsaro na Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kebbi da sojoji, ta yi nasarar halaka wasu dandazon ‘yan ta’adda yayin wani atisayen haɗaka a Dajin Gumki da ke Ƙaramar Hukumar Kangiwa a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa, an gudanar da atisayen ne da misalin ƙarfe 6:05 na safiyar ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026, wanda ya kuma taimaka wajen ƙwato wasu bindigogi, alburusai, babura da wasu ababe da ake zargin na ‘yan ta’addan ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kebbi, SP Bashir Usman da Mai magana da yawun Shiyya ta 8 ta Rundunar Sojin Nijeriya, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ne suka tabbatar da ukuwar lamarin a mabambanta sanarwa. A cewar sanarwar ‘yan sanda, jami’an tsaron sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan yayin “atisayen sharewa”, inda suka yi nasarar halaka wasu daga cikin su.

Ababen da aka ƙwato daga atisayen sun haɗa da bingar ƙirar PKT tare da alburusai guda 174, bindigar AK-47 tare da alburusai 14, wayoyin hannu biyu, babura huɗu, kakin sojin, takalmi sau-ciki da wasu kayan tsafi.

Rundunar ta kuma ce, yankin yana halin aminci yayin da jami’an tsaro suke cigaba da sintiri da nufin kawar da ‘yan ta’adda a dajin da yankunan da ke kewaye da shi.

A gefe guda kuma, sanarwar sojoji ta ce cikin ababen da aka ƙwato baya ga waɗanda ‘yan sanda suka faɗa, akwai tsabar kuɗi N87,000 da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum.

Dajin na Gumki, wanda ke yankin iyakar Nijeriya da Nijar, sanannen waje ne da ‘yan bindiga da mayaƙan Lakurawa suke amfani da shi a matsayin mafaka.

By Babaji

Leave a Reply