Mai Martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, ya karɓi tawaga daga ƙananan hukumomin Dutsi da Sabuwa, wadda ta kai ziyara a masarautar domin yin gaisuwa da Jinjina.
Tawagar ta yi godiya da jinjina ga mai martaba bisa naɗa sabbin hakimai da za su wakilci al’ummar ƙananan hukumomin biyu, Alh.Ibrahim Bello, wanda aka naɗa a matsayin Kogon Katsina, Hakimin Sabuwa, da Alhaji Abba Lawal Sani, wanda aka naɗa Gabasawan Katsina, Hakimin Dutsi.
Da yake jawabi a madadin al’ummar ƙaramar hukumar Sabuwa, Hon. Sagir Tanimu ya yaba wa Mai Martaba bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci da daidaito a cikin al’amuran masarautar.
Ya kuma yi wa sarki addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, yana mai tabbatar da cewa al’ummar Sabuwa za su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga Masarautar Katsina tare da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da ci gaba da zaman lafiya.
Shi ma shugaban ƙaramar hukumar Dutsi, Hon. Rabo Ado Kayawa, ya bayyana godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Katsina, tare da yi masa fatan alheri da addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya.
Ya ce al’ummar Dutsi sun nuna farin cikinsu da naɗa Alhaji Abba Lawal Sani a matsayin hakimin Dutsi, tare da fatan zai yi amfani da wannan dama wajen wakiltar al’ummar yankin cikin adalci da gaskiya.
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman , ya ja hankalin sabbin hakiman da su yi koyi da kyawawan halayen magabatansu, musamman wajen tabbatar da adalci, gaskiya da amana.
Mai Martaba ya kuma shawarce su da su ji tsoron Allah a dukkan al’amuransu, domin samun kariya da dacewa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa “adalci shi ne ke sa talakawa su yi biyayya ga shugabanninsu, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.”
A ƙarshe, an rufe taron da addu’ar Allah ya kawo zaman lafiya a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya, tare da roƙon Allah ya ƙara wa Mai Martaba Sarkin Katsina lafiya da ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da jagorantar Masarautar.
