Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar “yan sanda a Katsina ta tallafa da Naira miliyan 28 ga ‘yan sanda 25 da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki.
Da yake miƙa chakin kuɗin ga Iyalan mamattan CP Ali Umar Fage ya ce wannan tsare ne na shugaban ‘yan sanda na ƙasa na kula da jin daɗin iyalan ‘yan sanda da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki.
CP Fage ya yi ta’aziyar ‘yan sandan da suka rasu tare da bayyana su matsayin jarumai da suka sadaukar da kai wajan bautawa ƙasa inda yayi fatan Allah masu rahama.
Ya ja hankalin iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace da kuma duba buƙatar su na yau da kullum domin magancewa, ya yabawa shugaban ‘yan sanda na ƙasa AIG Olatunji Rilwan Disu wajen kula da jin daɗi da tabbatar da cewa sadaukar da rayuwar su wajan bautawa ƙasa bai tafi a banza.
Da yake jawabi a madadin iyalan ‘yan sandan da suka rasu Alkasim Salisu ya gode wa shugaban ‘yan sanda na ƙasa da CP Ali Umar Fage bisa wannan karamcin da aka nuna masu,yana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da tallafin wajan inganta rayuwar iyalan.
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta ce ba zata gajiya ba wajen kula da inganta rayuwar jami’an ta a fadin jihar.
